TCN Zai Magance Matsalolin Wutar Lantarki, An Fara Inganta Manyan Tashoshi 3
- Kamfanin wutar lantarki ya fara aikin inganta tashoshin wutar lantarki da $20m da aka karbo daga Bankin Duniya
- An fara aikin inganta tashoshin lantarki uku da ke Legas, kuma ana sa ran taho da aikin jihohin Kano da Adamawa
- Manajan daraktan TCN, Sule AbdulAzizi, ya shaidawa manema labarai cewa, aikin wani bangare ne ya rage rashin wuta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Lagos - Kamfanin rarraba tantarki na kasa (TCN), ya bayyana cewa zai dauki wasu manyan matakai uku domin kara wadata ‘yan kasa da hasken wuta.
Kamfanin ya bayyana matakan a lokacin da ake fama da matsalolin karancin hasken wutar, ko rashinsa a wasu sassa kasar nan.
Jaridar Premium Times ta wallafa cewa Manajan daraktan TCN, Sule AbdulAziz, ya shaidawa manema labarai a Legas cewa za a samu karin turansufoma manya uku a Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wuraren da TCN zai kara turansufoma
Jaridar Punch ta wallafa cewa TCN za ta samar da sababbin turansufoma da za a girka a manyan tashoshi guda uku da ke Alausa, Ota, da Alagbon, duka a jihar Legas.
Wannan na daga cikin shirin gwamnati, wanda Bankin Duniya ya bayar da Dala miliyan 200 domin taimakawa kasar nan wajen wadata jama’arta da hasken wutar lantarki.
TCN zai inganta wutar lantarki a Kano
Shugaban TCN, Sule AbdulAziz ya nanata cewa samar da wadatacce kuma tsayayyen wutar lantarki shi ne kashin bayan cigaba da bunkasar tattalin arziki.
Ya bayyana cewa inganta wutar lantarki da ake yi a Legas somin tabi ne, domin ana shirin fara makamancin gyare-gyaren a jihohin Kano da Adamawa don inganta rarraba hasken wutar.
An yi alkunuti saboda rashin wutar lantarki
A wani labarin, kun ji cewa wasu daga cikin masu kananan masana'antu a Kano su ka gudanar da sallar kunuti saboda yadda rashin wutar lantarki ke kara kamari a jihar.
'Yan kasuwar da su ka fito daga yankin Dakata sun shaida cewa sun kai kukansu ga Allah SWT bayan shafe akalla kwanaki 70 ba tare a ganin ko kyallin hasken wutar lantarki ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng