An Kama Rikakken 'Dan Damfara da Matashi Mai Satar Matar Aure

An Kama Rikakken 'Dan Damfara da Matashi Mai Satar Matar Aure

  • Rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta kama wanda ake zargi da damfarar mutane sama da Naira miliyan 2.7, Bishir Abdullahi
  • An samu Bishir Abdullahi da katunan cire kudi na ATM guda 14 da ya ke amfani da su wajen damfarar mutane a bankuna
  • Rundunar ta samu nasarar cafke wasu masu laifi da suka hada da masu satar mutane, fashi da makami da satar kayan gwamnati

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Katsina - Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta sanar da kama wani shahararren dan damfara mai suna Bishir Abdullahi.

An kama Abdullahi ne a wani reshen bankin First Bank da ke Tudun Katsira, bayan wani dan sanda ya gano ayyukan damfararsa.

Katsina
An kama dan damfara a Katsina. Hoto: Nigerian Police Force
Asali: Facebook

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa Abdullahi ya shahara wajen sauya katunan ATM na mutane domin cire kudi daga asusun ajiyarsu.

Kara karanta wannan

TCN zai magance matsalolin wutar lantarki, an fara inganta manyan tashoshi 3

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda matashi ke damfara a Katsina

Bayanai sun nuna cewa Bishir Abdullahi ya yi amfani da katunan ATM 14 wajen cire kudi tsakanin N49,000 zuwa N900,000 daga asusun mutane daban-daban.

Rundunar ‘yan sanda ta bayyana cewa an gano ya sace jimillar Naira miliyan 2.7 daga wurin wadanda ya damfara.

Daily Post ta wallafa cewa hakan ya biyo bayan bincike kan ayyukan damfararsa a cikin bankuna da kuma bayanan wadanda abin ya shafa.

Matashi ya sace matar aure a Katsina

Rundunar ‘yan sandan Katsina ta sanar da wasu nasarorin da ta samu wajen yaki da laifuffuka a jihar, wadanda suka hada da kama masu garkuwa da mutane, barayi da 'yan fashi.

An kama wani da ake zargi da garkuwa da mutane mai suna Mu’azu Yunusa a Kankia, wanda aka ce ya yi garkuwa da mutane biyar, ciki har da ‘yar shekara 14 da wata matar aure.

Kara karanta wannan

Bayan shawarar Kwankwaso, Jibrin Kofa ya nemi afuwa kan goyon bayan kudirin haraji

An bayyana cewa Mu’azu Yunusa ya jagoranci sace mutane a garin Mai Danko a lokuta daban-daban a watan Oktoba da Nuwamba na shekarar 2024.

An tarwatsa 'yan ta'adda a jihar Imo

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar ‘yan sanda a jihar Imo ta samu nasarar wargaza maboyar ‘yan ta’adda a ƙaramar hukumar Okigwe.

Kwamishinan ‘yan sanda jihar, Aboki Danjuma ya ce sun kama wasu manyan masu laifi a yayin farmakin da suka kai kan 'yan ta'addar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng