'Babu Hannun Lakurawa': An Kalubalanci Yan Sanda da Bama Bamai Suka Hallaka Mutane
- Wasu masana sun kalubalanci kwamishinan yan sanda a Zamfara kan sanarwar da ya fitar game da tashin bama-bamai
- Rahotanni sun tabbatar cewa kwamishinan yan sanda, Muhammad Shehu Dalijan ya zargi Lakurawa da dasa bama-baman a yankin Dansadau
- Hakan ya biyo bayan tashin bama-bamai da ya yi ajalin mutane da dama a karamar hukumar Maru da ke jihar Zamfara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Zamfara - Masana sun yi magana kan zargin yan kungiyar Lakurawa da dasa bama-bamai a jihar Zamfara.
Majiyoyi sun musanta rade-radin cewa Lakurawa ne suka dasa bama-baman bayan sanarwar kwamishinan yan sanda.
An hallaka mutane bayan dasa bam a Zamfara
Shafin Zagazola Makama shi ya tabbatar da haka a shafin X, ya ce an kalubalanci kwamishinan yan sanda kan haka.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan na zuwa ne bayan rasa rayukan mutane da dama sanadin dasa bam din a kan hanyar Dansadau a karamar hukumar Maru da ke jihar Zamfara.
Kwamishinan yan sanda a jihar Zamfara, Muhammad Shehu Dalijan ya fitar da sanarwar inda ya zargi yan Lakurawa da dasa bama-baman.
Zamfara: An zargi yan sanda da yaudarar al'umma
Sai dai wasu masana sun musanta sanarwar kwamishinan inda suka tabbatar da cewa babu Lakurawa a yankin jihar Zamfara.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa Lakurawa sun fi karfi a wasu yankunan jihar Sokoto da Kebbi da iyakar Nijar tun bayan fatattakarsu da sojoji suka yi.
Masana sun kalubalanci kwamishinan, suka ce sanarwar da ya bayar za ta yaudari al'umma ne kawai.
"Babu wata hujja kan cewa Lakurawa ne suka dasa bama-baman, mafi yawan ayyukansu a Sokoto da Kebbi suke yi."
"Sannan babu wani rahoto da yake alakanta kungiyar da amfani da abubuwan fashewa tun bayan zuwansu yankin Arewa maso Yamma."
- Cewar majiyoyi
An yi arangama kan neman kujerar Sububu
Kun ji cewa wasu rahotanni sun tabbatar da cewa fada ta barke tsakanin bangarorin yan ta'adda guda biyu a jihar Zamfara.
Ana hasashen an kaure da fadan bayan kisan kanin shugaban 'yan bindiga, Najaja da ake kira Dan'auta a jihar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng