Injin Jirgin Mataimakin Gwamna Ya Kama da Wuta a Sararin Samaniya

Injin Jirgin Mataimakin Gwamna Ya Kama da Wuta a Sararin Samaniya

  • Mataimakin gwamnan Borno, Dr. Usman Kadafur da wasu fasinjoji 70 sun tsira daga hadarin jirgin sama a jihar
  • An ruwaito wani jirgin Max Air ya gamu da tangarda a lokacin da ya lula sararin samaniya a hanyarsa ta zuwa birnin Abuja
  • Amma ya yi saukar gaggauwa a filin jirgin Maiduguri da aka samu hadarin da ya sanya daya daga cikin injinansa ya kama da wuta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Borno - Wani jirgin saman Max Air da ke dauke da mataimakin gwamnan Borno, Dr. Usman Kadafur, tare da fiye da fasinjoji 70, ya samu babbar matsala a sararin samaniya.

Injin jirgin ya kama da wuta jim kadan bayan ya lula sama, inda ma’aikatan jirgin su ka shaida cewa lamarin ya faru ne kusan mintuna 10 bayan tashin jirgin, wanda ya nufi Abuja.

Kara karanta wannan

TCN zai magance matsalolin wutar lantarki, an fara inganta manyan tashoshi 3

Max Air
Injin jigrin Max Air ya kama da wuta a sararin sama Hoto: Max Air Ltd
Asali: Facebook

Zagazola Makama ya wallafa a shafinsa na X cewa jirgin ya yi saukar gaggawa a filin jirgin sama na Maiduguri a ranar Laraba domin tsiratar da fasinjojin da ke a cikinsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin kamawar injin jirgin sama da wuta

Rahotanni daga ma’aikatan Max Air sun bayyana cewa jirgin ya bugi tsuntsu jim kadan bayan ya tashi, wanda ya haifar da gobarar injinsa.

Matukin jirgin ya dauki matakin gaggawa ta hanyar kashe injin da ya lalace, sannan ya yi nasarar sauke jirgin a Maiduguri.

An samu asara a gobarar jirgin?

Rahotanni sun bayyana cewa dukkanin fasinjoji da ma’aikatan jirgin sun tsira da lafiyarsu, wanda aka danganta da yadda matukin ya dauki matakan gaggawa.

Tuni Max Air ya aika wani jirgin zuwa Maiduguri wanda ya kwashe dukkanin fasinjojin da suka makale zuwa Abuja, wanda ya tashi daga Maiduguri da misalin karfe 11.00 na dare.

Jirgin sama ya samu matsala a Abuja

Kara karanta wannan

Kudirin harajin Tinubu: Kwamitin majalisa zai zauna da babban lauyan gwamnati

A wani labarin, mun ruwaito cewa jirgin sama na Air Peace ya samu matsala a lokacin da ya ke tsaka da shirin tashi daga filin jirgi a babban birnin tarayya Abuja zuwa Legas.

Kamfanin sufurin jiragen sama na Air Peace ya bayar da tabbacin afkuwar lamarin, inda ya kara da cewa an samu tangarda ne bayan jirgin ya ci karo da wata tsuntsuwa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.