Bayan Fafutukar Shekaru 22: Kotu Ta ba Malamin da Aka Kora a Aiki Nasara

Bayan Fafutukar Shekaru 22: Kotu Ta ba Malamin da Aka Kora a Aiki Nasara

  • Malamin Jami’ar Uyo, Inih Ebong da aka sallama ba tare da adalci ba shekaru 22 da suka wuce ya samu nasara a kotu
  • Kotun daukaka kara ta tabbatar da hukuncin kotun masana’antu na dawo da shi aiki tare da biyan dukkan hakkokinsa
  • Malamin ya gode wa Femi Otedola da lauyan kare hakkin dan Adam, Inibehe Effiong bisa goyon bayan da suka ba shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Akwa Ibom - Bayan shafe shekaru 22 yana fafutuka a kotuna, Inih Ebong, wanda aka kora daga Jami’ar Uyo bisa zalunci ya samu nasara.

Kotun daukaka kara ta Calabar ta yi watsi da bukatar jami’ar ta dakatar da aiwatar da hukuncin wata kotu a 2020, wanda ya umurci a dawo da malamin tare da biyan dukkan hakkokinsa.

Kara karanta wannan

An kashe 'yan bindigar da suka daure babban ma'aikaci a cikin rami

Malamin jami'a
Malamin jami'ar Uyo ya samu nasara a kotu bayan shekaru 22. Hoto: Cletus Ukpong
Asali: UGC

Lauyan Ebong, Nse William, ya tabbatar wa da jaridar Premium Times cewa wannan hukunci ya kawo ƙarshen shari’ar, yana mai godiya ga Allah.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin korar malami a jami'ar Uyo

An kori Inih Ebong daga Jami’ar Uyo a shekarar 2002 bisa zalunci inda aka ce ya bar aikin sa ba tare da izini ba.

Malamin jami'ar, wanda aka san shi da yawan sukar rashin adalci da cin hanci a makarantar, ya fara fafutukar neman adalci tun daga lokacin har zuwa yanzu da kotu ta tabbatar da hakkin sa.

“Ko shugaban jami’ar yana so ko baya so, dole ne a biya ni hakkina. Wannan ita ce kaddarar sa.”

- Inih Ebong

Ebong ya yi godiya ga al'umma

Mista Ebong ya nuna farin cikinsa game da hukuncin tare da gode wa ‘yan Najeriya da suka tsaya tare da shi cikin gwagwarmayar.

Ya yi godiya ta musamman ga attajirin Najeriya, Femi Otedola, wanda ya dauki nauyin maganin sa, da kuma lauya Inibehe Effiong, wanda ya yi tattaki daga Lagos zuwa Uyo domin tallafa masa.

Kara karanta wannan

Atiku ya dura a kan 'yan sanda, ya soki yadda aka kama mai adawa da gwamnati

Iyalan Ebong sun nuna farin ciki

Matar Mista Ebong mai suna Uduak ta bayyana yadda wannan gwagwarmayar ta yi tsawo tun lokacin da ta haifi ‘yarta ta farko.

Ta ce yanzu haka yarinyar ta na da shekara 21 tana karatun jami’a, kuma dukkan ‘ya’yansu sun kasance masu goyon baya ga gwagwarmayar.

Babbar kotu ta yi hukunci a Kano

A wani rahoton, kun ji cewa babbar kotun Kano ta ba da umarni kan hana ƙananan hukumomin jihar kuɗinsu a asusun tarayya.

Rahotanni na nuni da cewa kotun ta dakatar da Akanta Janar na tarayya, CBN da hukumar RMAFC hana ba ƙananan hukumomin Kano kuɗi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng