Faduwar Darajar Naira Ya Sake Rikirkita Komai, Bashin Najeriya Ya Karu da N30trn
- Basussukan da ake bin Najeriya daga ƙasashen ketare na cigaba da karuwa saboda faduwar darajar Naira duk wayewar gari
- A watan Yunin 2023 da farashin dala ke N770 bashin yana N43.15trn kafin faduwar darajar Naira wanda ya kai N1,470 a watan Yunin 2024
- Bashin da ake bin kasar yana nan yadda yake a farashin dala amma ya yi mummunan tashi da N30trn saboda ragurgujewar darajar Naira
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Cigaba da faduwar darajar Naira a Najeriya ya jawowa kasar mummunan asara ta ɓangarori da dama.
Karyewar darajar Naira ya kara bashin Najeriya a ketare zuwa N30.03trn daga watan Yunin 2023 zuwa watan Yunin 2024.
Faduwar darajar Naira ya sauya bashin Najeriya
Rahoton Punch ya tabbatar da cewa duk da raguwar bashin da ake bin kasar a kudin Dala, amma faduwar darajar Naira ya sake kara bashin da ake binta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wani rahoto da hukumar kula da basussuka (DMO) ta fitar ya ce bashin Najeriya a watan Yunin 2023 ya kai N43.15trn.
A watan Yunin 2024, darajar Naira ta fadi da 47% wanda farashin dala ya kai har N1,470 a kasuwanni.
Yadda bashin Najeriya ya karu a shekara 1
Rahotanni suka ce idan da har yanzu farashin dala yana N770 kamar a watan Yunin 2023 da bashin da ake bin kasar ba zai wuce N33trn ba.
Sai dai ragurgujewar darajar Naira a Najeriya ya karawa kasar bashin da ya kai N30.02trn cikin shekara daya kacal.
Duk da haka tulin bashin da ake bin kasar yana nan yadda yake amma farashin dala na nan yadda aka lissafa tun farko.
Asarar da Najeriya ta yi a shekaru 3
Kun ji cewa Gwamnatin Najeriya ta tafka asarar N13.2tn sakamakon aiwatar da manufofinta na tallafin canjin kudin waje a shekaru uku.
Rahoton cigaban Najeriya (NDU) da Bankin Duniya ya fitar ya nuna cewa Najeriya ta rasa makudan kudin ne daga 2021 zuwa 2023.
A watan Oktoban 2024, Ministan kuɗi, Wale Edun, ya sanar da cewa gwamnati ta kawo karshen tallafin fetur da na musayar kudaden waje.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng