Fitaccen Mawakin Kannywood Ya Rigamu Gidan Gaskiya, Ali Nuhu Ya Yi Magana

Fitaccen Mawakin Kannywood Ya Rigamu Gidan Gaskiya, Ali Nuhu Ya Yi Magana

  • Allah ya karbi rayuwar shahararren mawakin Hausa, El-Muaz Birniwa a daren ranar Alhamis, 5 ga watan Disambar 2024
  • Abdul M Shareef, jarumi a masana'antar Kannywood ne ya sanar da rasuwar El'Mua'z tare da yin adduar Allah Sarki ya jikansa
  • Masana'antar fina finan Hausa ta shiga jimami kan wannan rasuwa, inda jarumai da daraktoci suka mika sakon ta'aziyya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kaduna - Masana'antar shirya fina finan Hausa ta fada cikin tashin hankali bayan samun labarin rasuwar fitaccen mawaki, El-Muaz Birniwa.

El-Muaz Birniwa ya shafe shekaru da dama a masana'antar nishadi ta Arewa, inda ya fi kwarewa a fannin wakokin siyasa, soyayya da zamantakewa.

Allah ya yiwa El-Muaz Birniwa rasuwa
Allah ya karbi rayuwar fitaccen mawakin Kannywood, El-Muaz Birniwa. Hoto: elmuaz
Asali: Instagram

Shahararren jarumin Hausa, Abdul M Shareed ne ya sanar da rasuwar El'Muaz Birniwa a shafinsa na Instagram.

Kara karanta wannan

Birniwa: Bidiyon karshe na fitaccen mawakin Kannywood kafin mutuwa ta dauke shi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Maishadda ya sanar da cewa:

"InnalilLahi Wa'inna ILaihi Raji'un. Allah ya yiwa El'Muaz Birniwa rasuwa.
"Allah ka jikan wannan bawa naka. Ya hayyu ya ƙayyum ka sa Aljannah ce makomarsa. Amin s. Amin."

Jarumai da mawaka sun yi ta'aziyya

Legit Hausa ta tattaro sakonnin ta'aziyya da jarumai da mawakan Kannywood suka wallafa a shafukansu na sada zumunta game da rasuwar El-Muaz Birniwa.

A shafinsa na Instagram, fitaccen jarumi, Ali Nuhu, ya wallafa cewa:

"Allah ya jikanka da rahama, ya sa mutuwa hutu ne a gareka."

Shalelen Mawaka, kuma na kusa da marigayi El'muaz, ya wallafa a shafinsa na Instagram cewa:

"Innalillahi wa inna ilaihi raji’un. Ya Allah mun tuba, ya Allah ka gafarta ma wannan bawa naka, ka bashi Aljannah. Kai duniya Allah kayi mana gafara, Allah ka jikan MU’AZU."

Babban mai ba da umarni, Sadiq N Mafia, ya wallafa a shafinsa na Instagram cewa:

Kara karanta wannan

Atiku ya dura a kan 'yan sanda, ya soki yadda aka kama mai adawa da gwamnati

"Na dade ina gani kuma ina jin mutuwa kuma na san kowa da lokacin sa, amma ban taba jin mutuwa irin na dan uwa, abokin shawara, abokin arziki irin taka Elmuaz Birniwa ba.
"Fata na kawai Allah ya jikanka da rahama Allah ya gafarta maka, kai masoyin Annabi Mohammad (S.A.W) ne kowa ya shaida, kai mai taimakon na kasa da kai ne kowa ya shaida, baka da hasada. Ya Allah ga bawan ka, ka fi mu sanin komai."

Mahaifiyar jarumar Kannywood ta rasu

A wani labarin, mun ruwaito cewa mahaifiyar fitacciyar jarumar Kannywood kuma tauraruwa a shirin 'Allura Cikin Ruwa', Ruky Alim ta rigamu gidan gaskiya.

Jarumai da kuma abokan sana'ar Ruky Alim sun taya ta alhini da jimamin wannan babban rashi bayan sanarwar mai shirya fina finai, Abubakar Bashir Maishadda.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.