Bayan Shawarar Kwankwaso, Jibrin Kofa Ya Nemi Afuwa kan Goyon Bayan Kudirin Haraji

Bayan Shawarar Kwankwaso, Jibrin Kofa Ya Nemi Afuwa kan Goyon Bayan Kudirin Haraji

  • Dan majalisa mai wakiltar Kiru da Bebeji, Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa ya musanta cewa ya goyi bayan kudirin gyaran haraji dari bisa dari
  • Kofa ya bayyana cewa ba zai taba mara baya ga duk wata doka ko kudiri da zai cutar da mazabarsa, Kano, Arewa ko Najeriya baki daya ba
  • Dan majalisar tarayyar ya nemi afuwar al’umma tare da tabbatar da jajircewarsa wajen kare muradun yankin Arewa da na kasa baki daya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Dan majalisa mai wakiltar kananan hukumomin Kiru da Bebeji, Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa ya bayyana cewa ba ya goyon bayan kudirin gyaran haraji dari bisa dari.

A wata sanarwa da ya fitar, ya ce yana amfani da matsayinsa domin kare muradun mazabarsa, Arewa da Najeriya baki daya.

Kara karanta wannan

Gwamna ya raba tallafin miliyoyi domin bunkasa kananan sana'o'i

Jibrin Kofa
Kofa ya nemi afuwa kan kudirin haraji. Hoto: Abdulmumini Jibrin Kofa
Asali: Facebook

Legit ta gano bayanin da Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa ya yi ne a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matsayar Jibrin Kofa kan kudirin haraji

Hon. Jibrin Kofa ya ce abin da ya fada shi ne, 'yan majalisar Arewa su yi amfani da rinjayensu wajen goyon bayan kudirorin da za su amfani yankinsu.

Ya kara da cewa cewa akwai abubuwa masu amfani a cikin kudirin, amma dole a gyara waɗanda za su iya cutar da yankin Arewa kafin a amince da su.

Kofa ya nemi afuwa kan kudirin haraji

Hon. Jibrin Kofa ya nemi afuwar duk wanda kalamansa suka ɓatawa rai, musamman shugabannin Arewa da sauran al’umma.

Ya kuma gode wa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Alƙali Abubakar Salihu Zaria bisa shawarwarinsu, tare da yi musu fatan alheri.

Jibrin Kofa zai kare muradun Arewa

Kara karanta wannan

Siyasar Kano: Barau ya bukaci majalisa ta mayar da sunan Yusuf Maitama a jami'ar FUE

Dan majalisar yi alkawarin yin duk abin da zai iya domin ganin ba a cutar da yankin Arewa ba a duk wani kudiri da za a gabatar.

A cewarsa, zai ci gaba da tsayawa tsayin daka wajen kare muradun mazabarsa da na Najeriya gaba ɗaya, kamar yadda ya saba a baya.

Tinubu ya yi magana kan kudirin haraji

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ce za a tabbatar da adalci a kan kudirin haraji da ake ce-ce-ku-ce a kansa.

Ministan yada labarai, Mohammed Idris ya bayyana cewa gwamnati ta buɗe kofa domin sauraron korafin yan Najeriya a kan kudirin harajin Bola Tinubu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng