ACF: Kungiyar Dattawan Arewa Ta Lashe Amanta game da Dakatar da Shugabanta kan Zaben Tinubu

ACF: Kungiyar Dattawan Arewa Ta Lashe Amanta game da Dakatar da Shugabanta kan Zaben Tinubu

  • Daga karshe, Kungiyar Arewa Consultative Forum ta janye dakatarwar da ta yi wa shugabanta, Mamman Mike Osuman
  • Kungiyar ta ce an samu maslaha bayan tsoma baki da kwamitin sulhu da zaman lafiya ya yi kan lamarin da ya faru
  • Wannan na zuwa ne bayan Osuman ya ce yan Arewa dan yankinsu za su goyawa baya a zaben 2027, ya caccaki Bola Tinubu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kaduna - Kungiyar Arewa Consultative Forum (ACF) ta dawo da shugabanta da ta dakatar kan kalamansa.

Kungiyar ACF ta janye dakatarwar bayan daukar mataki kan Mamman Mike Osuman da ya yi katobara game da zaben 2027.

Kungiyar ACF ta dawo da shugabanta da ta dakatar bayan sukar Tinubu
Kungiyar ACF ta janye dakatar da shugabanta, Mamman Mike Osuman. Hoto: Arewa Consultative Forum.
Asali: Facebook

Tinubu: An dakatar da shugaban kungiyar ACF

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren kungiyar, Murtala Aliyu ya fitar da jaridar The Nation ta samu.

Kara karanta wannan

Gwamna ya fadi yadda aka kubutar da kananan yara 4 da 'yan bindiga suka sace a Kaduna

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na zuwa ne bayan Mike Osuman ya yi wasu kalamai da kungiyar ke ganin ya saba ka'ida ba tare da yawunsu ba.

Osuman a cikin wata sanarwa ya ce yan Arewa ba za su zabi Bola Tinubu ba a zaben 2027, ya ce 'dan yankinsu za su goyawa baya.

Kalaman Osuman bai yi wa kungiyar dadi ba, ta ce ya yi maganar ba tare da saninta ba kuma ta ce ya yi hakan ne a karan kansa, cewar Channels TV.

ACF ta janye dakatarwar da ta yi wa shugabanta

Murtala Aliyu ya tabbatar da cewa an shawo kan matsalar cikin lumana bayan shiga lamarin da kwamitin zaman lafiya na kungiyar ya yi.

"Bayan dakatar da shugaban kungiyar ACF, Mamman Mike Osuman bayan furta wasu kalamai na siyasa da ba su dace da tsarinmu na rashin nuna bangaranci a siyasa ba."
"Kwamitin zaman lafiya na kungiyar karkashin jagorancin Dr. Mahmud Yayale Ahmad ya shiga lamarin da wasu masu ruwa da tsaki."

Kara karanta wannan

'Ba a fahimci abin ba': Sanata Barau ya yi karin haske kan haraji, ya fayyace komai

"Daga bisani an kawo karshen matsalar cikin lumana duba da muradun al'ummar Arewa, kuma an janye dakatarwar da aka yi."

- Murtala Aliyu

Kungiyar ACF ta wanke Tinubu kan matsalolin Arewa

Kun ji cewa ana ta zargin Shugaba Bola Tinubu kan matsalolin Arewa, kungiyar ACF ta yi martani mai tsauri kan matsalolin yankin.

Shugaban kungiyar Arewa Consultative Forum, Mamman Mike Osuman ya ce matsalolin Arewa laifin shugabanninta ne.

Osuman ya ce ba za su daurawa Tinubu laifi ba kan abubuwan da ke faruwa duk da tsare-tsarensa ba su dace da yankin ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.