'Dan Kano Ya Hargitsa Zaure, Ya Nemi Mataimakin Shugaban Majalisa Ya Bar Mukaminsa

'Dan Kano Ya Hargitsa Zaure, Ya Nemi Mataimakin Shugaban Majalisa Ya Bar Mukaminsa

  • Dan majalisar Kano, Dr. Ghali Mustapha Tijjani ya zargi mataimakin kakakin majalisa, Benjamin Kalu da wuce gona da iri
  • Ya bayyana takaicin yadda Hon. Kalu ya shaidawa manema labarai cewa suna muradin a gaggauta tabbatar da kudirin haraji
  • Dr. Ghali Mustapha Tijjani da wasu daga cikin 'yan majalisa sun nemi Benjamin Kalu ya sauka daga mukamin da yake kai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Zaman majalisar wakilai na yau Laraba ya dauki zafi da 'dan majalisar Kano, Dakta Ghali Mustapha ya bukaci mataimakin kakakin majalisa, Benjamin Kalu ya bar mukaminsa.

Dakta Ghali Mustapha Tijjani, dan majalisar wakilai mai wakiltar Gaya/Albasu ya zargi Hon. Benjamin Kalu da bayar da bayanan karya a kan wasu daga cikin 'yan majalisa.

Kara karanta wannan

Atiku ya dura a kan 'yan sanda, ya soki yadda aka kama mai adawa da gwamnati

House
Dan majalisar Kano ya nemi Benjamin Kalu ya ajiye mukaminsa Hoto: House of Representatives
Asali: Twitter

A bidiyon da Leadership News ta wallafa, dan majalisar ya ce Benjamin Kalu ya wuce gona da iri wajen bayar da bayanan da ba haka su ke ba, kuma ya keta hakkinsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hon. Ben Kalu ya fusata 'yan majalisa

Bidiyon da Asad ya wallafa a shafinsa na X, ya nuna dan majalisar Kano, Dakta Ghali Mustapha Tijjani a fusace bisa rahoton da Benjamin Kalu ya ba 'yan jarida.

Mataimakin kakakin majalisar ya shaidawa manema labarai cewa, wadanda ke adawa da kudirin harajin Tinubu, yanzu sun dawo su na neman a tabbatar da ita.

"Wanan ya taba mutuci na, da na addini na, da na mutane na da yankin da na ke wakilta, wannan bai dace ba. Saboda haka kakakin majalisa, ina neman Benjamin Kalu ya sauka daga mukaminsa, ko a bincike shi."

'Yan majalisa sun goyi bayan Dakta Ghali

Bidiyon 'yan majalisar wakilai ya nuna yadda su ka rika tasowa su na bayyana cewa su na bukatar Benjamin Kalu ya bar mukaminsa saboda cin zarafin ofis.

Kara karanta wannan

"Ba talakawa ya kamata a tatsa haraji ba," Sanata Ibrahim ya kawo mafita

Guda daga cikin 'yan majalisar ya nemi a mika batun da kwamitin tsawatarwa ya binciki lamarin, sannan da dama daga 'yan majalisar sun nemi Hon. Kalu ya sauka.

'Yan majalisa sun yi watsi da kudirin haraji

A wani labarin, mun ruwaito yadda wasu daga cikin 'yan majalisar Kano su ka hade wuri guda wajen bayyana kin amincewa da kudirin harajin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.

'Yan majalisar sun tattauna a Kano karkashin jagorancin gwamnatin Abba Kabir Yusuf, daga bisani ne kuma su ka bayyana matsayarsu a kan batun kudirin harajin gwamnatin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.