Majalisar Dattawa ta Dakatar da Tattauna Kudirin Haraji, Ta Kafa Kwamitin Bincike

Majalisar Dattawa ta Dakatar da Tattauna Kudirin Haraji, Ta Kafa Kwamitin Bincike

  • Majalisar Dattawa ta kafa kwamitin da Sanata Abba Moro ke jagoranta domin tantance kudirin sauya fasalin haraji
  • Kwamitin zai yi aiki tare ma'aikatar sharia'a da wasu masu ruwa da tsaki domin warware batutuwan da ake takaddama a kai
  • Ana sa ran kwamitin zai gabatar da rahoto ga majalisar kafin a gudanar da sauraron ra'ayoyin jama’a kan kudirin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum

FCT, Abuja - Majalisar dattawa ta kafa kwamitin da zai tantance takaddun kudirin haraji da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya gabatar tun ranar 3 ga watan Oktoba, 2024.

Sanata Abba Moro, wanda ke wakiltar Benue ta Kudu, zai jagoranci kwamitin, wanda zai gudanar da bincike mai zurfi kan wuraren da ake samun rashin fahimta a kansu.

Kara karanta wannan

Rikicin cikin gida ya yi kamari a APC, an kafa kwamitin sulhu

Majalisa
Majalisa ta kafa kwamiti kan kudirin haraji. Hoto: Nigerian Senate
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa mataimakin shugaban majalisar, Sanata Barau I. Jibrin ne ya sanar da kafa kwamitin a zaman majalisar na yau Laraba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ruwaito cewa Sanata Barau ya ce aikin kwamitin ya hada da tuntubar gwamnati da sauran bangarori masu muhimmanci.

Aikin da kwamitin haraji zai yi a majalisa

Kwamitin karkashin jagorancin Sanata Abba Moro zai yi aiki da ma'aikatar shari'a, bangaren zartarwa, da sauran masu ruwa da tsaki domin warware batutuwan da ke cikin kudirin.

Sanata Barau I, Jibrin ya bayyana cewa an samu ce-ce-ku-ce kan kudirin haraji da aka gabatar, saboda haka kwamitin zai gabatar da rahoto ga majalisa kafin a fara sauraron ra’ayin jama’a.

Sanatocin da za su jagoranci kwamitin binciken

Rahoton Channels Television ya nuna cewa wallafa cewa daga cikin sanatocin da aka zabo a cikin kwamitin akwai Sanata Titus Zam daga Benue ta Yamma.

Kara karanta wannan

Gwamna ya ji kukan ƴar NYSC da malama ta lakadawa duka a Ilorin, ya dauki mataki

Haka zalika akwai Orji Uzor Kalu daga Abia ta Arewa, Sani Musa daga Neja ta Gabas, da Abdullahi Yahaya daga Kebbi ta Arewa.

Ana hasashen cewa kwamitin zai yi nazarin yadda sauye-sauyen harajin za su taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin kasa, tare da tabbatar da adalci ga daukacin ‘yan Najeriya.

Tinubu ya yi magana kan kudirin haraji

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi magana yayin da aka rika korafi kan kudirin harajin da ya gabatar da shi.

Ministan yada labarai, Mohammed Idris ya bayyana cewa shugaba Bola Tinubu zai saurari koken al'umma kuma za a yi wa kowane yanki adalci.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng