Yan Bindiga Sun Sace Kansila Tsakar Dare, Sun bi Gida Gida Suna Daukar Mutane
- Mutane tara, ciki har da kansila, Hon. Alaba Ope sun fada hannun ‘yan bindiga a Odo-Ape, karamar hukumar Kabba/Bunu a Kogi
- Satar mutanen ta biyo bayan kama wasu mutum uku a mako guda da ya gabata a yankin, ciki har da wani yaro dan shekara takwas
- Al’ummar yankin Odo-Ape sun bukaci taimako daga hukumomin tsaro da gwamnatin jihar domin kare rayuka da dukiyoyinsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kogi - Wasu ‘yan bindiga sun kai farmaki garin Odo-Ape da ke karamar hukumar Kabba/Bunu a jihar Kogi da tsakar daren ranar Talata.
Cikin wadanda aka sace har da kansila mai wakiltar mazabar Odo-Ape, Hon. Alaba Ope wanda aka ce an dauke shi a gidansa.
Vanguard ta wallafa cewa wani mazaunin yankin ya tabbatar da cewa ‘yan bindigar sun kai harin ne da misalin karfe 1 na dare.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Miyagun mutane sun sace kansila a Kogi
Rahotanni na nuni da cewa an sace mutane takwas da suka hada da kansila Alaba Ope a garin Odo-Ape na jihar Kogi.
Har ila yau, wani mutum mai suna Silas daga garin Agbadu wanda ke kusa da Odo-Ape ya fada hannun ‘yan bindigar a yayin farmakin.
An yi kira ga jami'an tsaro a jihar Kogi
Al’ummar yankin Odo-Ape sun yi kira ga hukumomin tsaro da gwamnatin Kogi da su taimaka wajen ceto wadanda aka sace da kuma kare yankin daga hare-hare.
Duk da cewa rundunar 'yan sandan jihar ba ta yi bayani ba, wata majiyar tsaro ta tabbatar da lamarin tana mai cewa an riga an dauki matakan gaggawa.
An bukaci jama’a su kwantar da hankali
Majiyar tsaron ta tabbatar wa jama’a cewa gwamnati na kokari kan lamarin tare da daukar duk wani mataki da ya dace domin tabbatar da tsaro a yankin.
Haka zalika an bukaci jama’a su ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum ba tare da fargaba ba.
An ceto dalibar jami'ar jihar Kogi
A wani rahoton, kun ji cewa hukumar NSCDC a Kwara ta ceto ɗaliba mai shekaru 19 da ke karatun yaren Turanci a jami'ar jihar Kogi bayan sace ta.
An ruwaito cewa an gano dalibar mai suna Fauziyah Mohammed ne tana yawo a tsirara a unguwar Ajegunle-Isale a birnin Ilorin na jihar Kwara.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng