Siyasar Kano: Barau Ya Bukaci Majalisa Ta Mayar da Sunan Yusuf Maitama a Jami'ar FUE
- Sanata Barau I Jibrin ya fara fafutukar a mayar da sunan Dan Masanin Kano, Yusuf Maitama Sule ga wata jami'a
- Ya fara daukar matakin ne bayan gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta cire sunan daga jami'ar NorthWest da ke jihar Kano
- Mataimakin shugaban majalisar dattawan, Barau Jibrin ya bayyana cewa tuni kudirin ya tsallake karatu na farko
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Sabanin siyasar Kano na shirin tsallakawa manyan makarantu, musamman kwanaki kadan bayan sauya sunan jami'ar Yusuf Maitama Sule zuwa tsohon sunanta.
A ranar Talata mataimakin shugaban majalisa, Barau I Jibrin ya gabatar da kudiri a gaban majalisa domin mayar da sunan Yusuf Maitama Sule ga jami'ar Ilimi ta tarayya (FUE).
A sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Barau I Jibrin ya bayyana farin cikin yadda kudirin da ya gabatar ya tsallake karatu na farko a zaman majalisar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ra'ayin 'yan FUE Kano na sauya sunan jami'ar
Wasu daga cikin daliban FUE sun bayyana cewa ba su damu da sunan da za a kira jami'ar ba, matukar ta na cigaba da koyo da koyarwa a cikin yanayi mai kyau.
Amina Alhassan ta shaidawa Legit cewa dama jami'ar ba ta da sunan wani, illa ana kiranta ne da 'Federal University of Education' kawai.
Ana zargin siyasa a sauya sunan jami'ar Kano
Wani babban malami a jami'ar FUE, Dr. Ibrahim Kabuga ya bayyana cewa ko da akwai siyasa a batun sauya sunan jami'ar, ba laifi ba ne.
Ya ce akwai takwarorin FUE a Kudancin kasar nan da ke dauke da sunayen manyan shiyyar da su ka bayar da gudunmawa wajen cigaban jama'arsu.
Kano: An sauya ranar bikin 'ya'yan Barau
A wani labarin, kun ji cewa an samu karin bayani kan dalilin da ya sa aka dauke bikin 'ya'yan Sanata Barau I Jibrin da na Alhaji Nasir Ado Bayero daga Kano zuwa Abuja.
Bayanin na zuwa bayan an fara zargin an sanya daurin auren 'ya'yan a fadar Nasarawa da Sarkin Kano 15, Aminu Ado Bayero ke zaune saboda wata manufa ta bambancin siyasa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng