Iftila'in Gobara: Yadda Aka Tafka Asarar Biliyoyin Naira a Wasu Jihohi 3 na Arewa
- Gobarar da aka yi a Yobe, Kwara da Taraba ta jawo asarar biliyoyin Naira yayin da 'yan kasuwa da dama suka rasa shagunansu
- An ce gobara ta kone shaguna 46 a kasuwar Bayan Tasha, Damaturu, sannan ta babbake bangaren masu kayan daki a Ilorin
- Yayin da ake zargin wutar lantarki ce ta ke haddasa gobarar, an ce wani babban wurin hutawa a Jalingo shi ma ya kone kurmus
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
An yi asarar dukiya ta biliyoyin Naira a jihohin Yobe, Kwara da Taraba sakamakon gobara da ta lakume kasuwanni, shaguna, da wurin hutawa.
A 'yan kwanakin nan, ana samun karuwar tashin gobara a kasuwannin Arewa da Kudu, kuma ana alakanta mafi yawan gobarar da wutar lantarki.
Gobara ta kone shaguna 46 a Yobe
A jihar Yobe, gobara ta kone shaguna 46 a kasuwar Bayan Tasha dake Damaturu, inda mutane 200 suka rasa hanyoyin samun abinci, inji rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gobarar ta fara ne da misalin karfe 2:30 na daren ranar Talata, kafin jami’an kashe gobara na jihar su dakile ta bayan shan wahalar samun hanyar shiga kasuwar.
Mataimakin gwamnan Yobe, Hon. Idi Barde Gubana, ya duba wurin da gobarar ta auku, yana mai zargin wutar lantarki da kasancewa silar tashin gobarar.
Channels TV ta rahoto Hon. Barde Gubana, ya sanar da bayar da gudunmuwar Naira miliyan 20 domin tallafawa bukatun gaggawa na wadanda abin ya shafa.
Motar katifa ta haddasa gobara a Kwara
A jihar Kwara, gobara ta lakume dukiya mai tarin yawa a kasuwar Ita Amodu dake titin Old Yidi, Ilọrin, inda kayan daki, tabarmi, da roba suka kone.
Kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kwara, Hassan Adekunle, ya ce gobarar ta tashi ne bayan wata tirela makare da katifu ta yi karo da karfen wutar lantarki a kasuwar.
Hukumar kashe gobara ta bayyana cewa katifun da ke makare a motar da suka kama da wuta ne suka jawo wutar ta bazu cikin sauri, a cewar rahoton Punch.
Lamarin dai ya ta'azzara ne bayan fashewar wata karamar cibiyar wutar lantarki da ke kusa da wurin, inda wutar da ta bazu zuwa gine-ginen da ke makwabtaka da kasuwar.
Gobara ta lalata wurin shakatawa a Taraba
A Taraba, jaridar Tribune ta rahoto cewa gobara ta kone dukiyar da ta kai darajar fiye da Naira biliyan ɗaya a Duchess Lounge dake kusa da filin wasa na Jolly Nyame a Jalingo.
Har yanzu dai ba a iya gano ainihin musabbabin tashin gobarar ba amma shaidun gani da ido sun ce gobarar ta tashi ne sakamakon maido wutar lantarki da karfi.
Gobarar ta lalata dukkanin dakunan da ke hawan farko na ginin, wanda ya ƙunshi babban dakin shakatawa na gama gari da kuma bangaren VIP da VVIP.
Mamallakin wurin shakatawar, Farfesa Joseph Albasu Kunini ya ce a yanzu haka an fara gyara wurin domin bikin cika shekaru uku a ranar 30 ga watan Disamba.
Gobara ta tashi a ofishin hukumar INEC
A wani labarin, mun ruwaito cewa mummunar gobara ta tashi a ofishin hukumar INEC da ke jihar Delta, inda aka yi asarar muhimman kayayyaki.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar ta shaida cewa gobarar ta lalata kusan akwatunan zaɓe 706, jakunkunan zaɓe 50, riguna 322, da sauran kayayyaki.
Asali: Legit.ng