Gwamnonin Arewa Sun Rage Adawa, Sun Gano Sassa Masu Amfani a Kudirin Harajin Tinubu
- Wasu daga cikin gwamnoni sun yabi sassan kudirin harajin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu da cewa zai amfani kasa
- Wannan na zuwa a lokacin da manyan Arewacin kasar nan ke adawa da kudirin da ake zargin zai takure shiyyar
- Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya ce ba a yi masu cikakken bayani a kan abin da kudirin ya kunsa da fari ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Nasarawa - Alamu sun bayyana na yadda gwamnoni su ka fara sassauta matsayarsu na adawa da kudirin harajin gwamnatin tarayya.
Da fari, wasugwamnonin Arewa sun yi tir da kudirin saboda wasu sassa da aka yi zargin za su tauye cigaban tattalin arzikin shiyyar.
Channels Television ta ruwaito gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule, na cewa da gwamnati ta yi masu cikakken bayanin kudirin, da ba ta fuskanci tirjiya daga garesu ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kudirin haraji: Dalilin gwamnoni na sassauta matsaya
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa gwamnonin Arewa sun ce ba su san da tsarin rabon harajin sayen kaya (VAT) na 60% a cikin kudirin haraji ba.
Gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule ya ce;
“Da ace Mista Taiwo Oyedele ya sanar da gwamnoni cewa sabon tsarin rabon harajin sayen kaya (VAT) na 60% don a samu daidaito, da ba za a sami rashin jituwa tun farko ba.
Gwamna Sule ya yabi kudirin harajin Tinubu
Gwamna Abdullahi Sule ya yaba da yadda kudirin harajin gwamnatin tarayya ya mayar da hankali ga daidaita harajin VAT da magance biyan haraji fiye da sau daya.
A taron da ya gudana domin bayanin kudirin harajin, shugaban kwamitin yi wa tsarin harajin kwaskwarima, Taiwo Oyedele, ya yi bayanin sassan da gwamnoni ba su fahimta ba.
'Yan majalisa sun yi tir da kudirin haraji
A baya kun ji cewa, wasu daga cikin 'yan majalisar tarayya da su ka fito daga jihohin Arewa sun amince da yin watsi da kudirin harajin shugaban kasa, Bola Tinubu.
Da ya ke jawabi bayan ganawar Sanatocin, Sanata Buba Umaru Shehu daga Bauchi ya ce dole su yi wa tufkar hanci daga yanzu, domin dakile barazanar kudirin ga Arewa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng