Gwamna Ya Dakatar da Kwamishina bayan Yi Wa Ma'aikata Barazana
- Gwamnan jihar Ebonyi, Francis Nwifuru ya ci gaba da nuna halin rashin son wasa da aiki daga wajen kwamishinoninsa
- Francis Nwifuru ya sake ɗaukar matakin ladabtarwa, ya dakatar da wani daga cikin kwamishinonin da ke aiki a ƙarƙashinsa
- Ya zuwa yanzu dai gwamnan ya dakatar da kwamishinoni guda huɗu bayan ya zarge su da aikata laifuffuka daban-daban
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Ebonyi - Gwamnan jihar Ebonyi, Francis Nwifuru, ya sake dakatar da wani kwamishina a gwamnatinsa, Uchenna Igwe.
Gwamna Francis Nwifuru ya dakatar da kwamishinan ne bisa zarginsa da rashin biyayya da kuma gazawa a aikinsa.
Gwamna Nwifuru ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ofishinsa na gidan gwamnati, a birnin Abakaliki, babban birnin jihar Ebonyi, cewar rahoton tashar Channels tv.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meyasa gwamna ya dakatar da kwamishinan?
Uchenna Igwe wanda shi ne kwamishinan ƙananan hukumomi da masarautu, an dakatar da shi ne nan take har sai baba ta gani a ranar Litinin, rahoton Daily Post ya tabbatar.
An tattaro cewa kwamishinan ya gaza wajen gudanar da aikin da gwamnan ya ba shi, kan biyan kuɗaɗen fansho na wani shugaban ƙaramar hukuma a jihar.
Gwamna Nwifuru ya dakatar da kwamishinoni
Dakatar da kwamishinan ya sanya adadin kwamishinonin da Gwamna Nwifuru ya dakatar a cikin a ƴan kwanakin nan sun kai guda huɗu.
A ƙarshen watan da ya gabata ne Gwamna Nwifuru ya dakatar da kwamishinonin kula da gidaje da raya birane, albarkatun ruwa har sai baba ta gani saboda rashin biyayya da yin sakaci da aiki.
Gwamnan ya kuma dakatar da kwamishinan lafiya na tsawon watanni uku saboda rashin iya aiki.
Gwamna ya yi wa ma'aikatan Ebonyi barazana
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Ebonyi, Francis Nwifuru ya sha alwashin dakatar da albashi da maye gurbin duk ma'aikacin da shiga yajin aikin NLC.
Gwamnan ya yi wannan barazana ne a wani jawabi kai tsaye da ya yi ga al'ummar Ebonyi ranar Litinin, 2 ga watan Disamba, 2024 a Abakaliki, babban birnin jihar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng