Majalisar Dattawa Ta Tabbatar da Naɗin Sabon Hafsan Rundunar Sojin Ƙasar Najeriya

Majalisar Dattawa Ta Tabbatar da Naɗin Sabon Hafsan Rundunar Sojin Ƙasar Najeriya

  • Majalisar Dattawa ta amince da naɗin hafsan rundunar sojin kasa ta Najeriya (COAS), Laftanar Janar Olufemi Oluyede
  • A zaman ranar Talata, 3 ga watan Disamba, kwamitin kula da rundunar sojin karƙashin Sanata Abdul'aziz Yar'adua ya gabatar da rahotonsa
  • Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Oluyede a matsayin muƙaddashin hafsan rundunar soji sakamakon rashin lafiyar Marigayi Lagbaja ƙafin rasuwarsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Majalisar dattawa ta tabbatar da nadin Laftanar Janar Olufemi Oluyede a matsayin hafsan rundunar sojin ƙasa ta Najeriya.

Majalisar ta tabbatar da naɗin sabon hafsan sojin ne a zamanta na yau Talata, 3 ga watan Disamba, 2024.

Bola Tinubu da Oluyede.
Majalisar dattawan Najeriya ta amince da bukatar Tinubu ta nadin hafsan sojin kasa Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

Hakan dai ya biyo bayan amincewa da rahoton da kwamitin kula da rundunar sojin kasa karkashin jagorancin Sanata Abdulaziz Yar'adua ya gabatar, Channels tv ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majalisar dattawa ta amince da nadin Oluyede

Kara karanta wannan

Ma'aikata za su cigaba da jira, Gwamnan Zamfara zai fara biyan mafi ƙarancin albashi a 2025

Bayan Sanata Abdul'aziz ya gabatar da rahoton, Majalisar dattawan ta amince da shawarwarin da kwamitin ya bayar gaba ɗaya nan take, rahoton Vanguard.

Shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya nada Laftanar Janar Oluyede a matsayin hafsan sojin kasa sakamakon rashin lafiyar Laftanar Janar Taoreed Abiodun Lagbaja.

Bayan rasuwar tsohon shugaban rundunar sojojin, shugaba Tinubu ya rubuta wasiƙa zuwa majalisar, inda ya buƙaci ta amince da Oloyede ya zama cikakken hafsan soji.

Yadda majalisa ta tantance sabon hafsan soji

Majalisar ta miƙa saƙon shugaban ƙasa ga kwamitin kula da rundunar sojin domin ya tantance shi tare da kawo rahoto da shawarwari.

A makon jiya, Sanata Abdul'aziz Yar'adua mai wakiltar Katsina ta Tsakiya, ya jagoranci tantance Laftanar Janar Oluyede a wani zaman sirri a zauren majalisar.

A zaman yau Talata, majalisar dattawan Najeriya ta tabbatar ɗa naɗin sabon hafsan rundunar sojojin Najeriya bayan gabatar da rahoton kwamiti Abdul'aziz. Yar'adua.

Kara karanta wannan

Kudirin sauya fasalin harajin Tinubu ya ƙara gamuwa da cikas a jihar Kano

Hafsan soji ya sha alwashin dawo da tsaro

A wani rahoton, kun ji cewa Laftanar Janar Olufemi Oluyede ya sha alwashin dawo da zaman lafiya idan aka tabbatar da shi a matsayin hafsan sojin ƙasan Najeriya.

Mukaddashin hafsan sojin ya ɗauki wannan alkawarin ne a wurin tantancewa a gaban kwamitin haɗin guiwa na majalisar tarayya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262