Sanata Barau: Matasan Arewa Sun Yi Gangami a Abuja, Sun Goyi Bayan Gyaran Haraji
- Matasa daga jihohin Arewa 19 sun yi gangami don nuna goyon baya ga Sanata Barau Jibrin a matsayin "Sardaunan zamaninmu"
- Gangamin ya biyo bayan amincewar majalisar dattawa na nemo masana da za su wayar da kan jama'a game da gyaran haraji
- Yayin da suka gargadi masu sukar Sanata Barau, matasan sun ce mataimakin majalisar dattawan na son ci gaban Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Matasa daga jihohin Arewa 19 sun yi gangami a kofar majalisar tarayya don nuna goyon baya ga mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin.
Sun bayyana Sanata Barau Jibrin a matsayin "Sardaunan zamaninmu" tare da gargadin masu sukarsa saboda ya goyi bayan a wayar da kai kan kudurorin gyaran haraji.
Gangamin ya biyo bayan matsayar da majalisar dattawa ta cimmawa na amfani da kwararru a wayar da kan jama'a kan gyaran harajin, inji rahoton Channels TV.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Barau: Matasan Arewa sun yi gangami a Abuja
A zaman majalisar, Sanata Barau ya jaddada cewa akwai bukatar ƙwararrun su wayar da kan sanatoci da 'yan Najeriya kan batun dokokin gyaran haraji.
Masu gangamin na ɗauke da kwalaye masu rubutu daban daban da suka hada da: "Barau: Sardaunan zamaninmu", "Barau jagoran Arewa", "A daina kai wa Barau hari".
Matasan sun yaba masa bisa goyon bayan da ya bayar wajen ƙaddamar da kudirin kafa hukumar raya yankin Arewa maso Yamma (NWDC).
Matasa sun jinjinawa Sanata Barau
Tsohon shugaban NANS, Tijjani Kabiru Mohammed, ya ce Sanata Barau bai nuna goyon baya ko adawa da dokokin gyaran haraji ba amma yana son a wayar da kai game da su.
Kwamared Tijjani ya ƙara da cewa, Sanata Barau yana ƙoƙarin tabbatar da ‘yan Najeriya sun fahimci dokokin harajin kafin a zartar da su don amfanin al’umma baki ɗaya.
Matasan sun bayyana cewa Sanata Barau shi ne sanata mafi kwazo a Arewa saboda goyon bayan talakawa da ya ke yi ta hanyar dokoki masu tasiri.
Sanata Barau ya magantu kan gyaran haraji
A wani labarin, mun ruwaito cewa mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin ya ce mutane ba su fahimci abin da ke kunshe a kudurin gyaran haraji ba.
Sanata Barau ya ce tsallake karatu na biyu da kudirin ya yi ba shi ne ke nufin cewa an gama ba inda ya ce akwai matakan da kudirin zai bi kafin a amince da shi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng