An Kama Mai Taimakon 'Yan Bindiga da Waya Suna Kira domin Karbar Kudin Fansa

An Kama Mai Taimakon 'Yan Bindiga da Waya Suna Kira domin Karbar Kudin Fansa

  • Rahotanni da suka fito daga jihar Kwara na nuni da cewa masu garkuwa da mutane sun sace wata uwa da ‘ya’yanta biyu a garin Ajase-Ipo
  • A wata nasara da suka samu, jami'an hukumar NSCDC sun kama wanda ake zargi da ba wa masu garkuwar bayanai, Abu Usman Soja
  • An ruwaito cewa masu garkuwa da mutanen sun nemi fansar Naira miliyan 50 wanda daga bisani sun rage kudin zuwa Naira miliyan 15

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kwara - A ranar 7 ga Nuwamba wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne suka sace wata mata da ‘ya’yanta biyu.

Rahotanni sun tabbatar da cewa an sace matar ne a garin Ajase-Ipo na karamar hukumar Irepodun a Jihar Kwara.

NSCDC
NSCDC ta kama mai taimakon 'yan bindiga. Hoto: Nigerian Security and Civil Defence Corps
Asali: Twitter

Leadership ta wallafa cewa bayan kwanaki, masu garkuwan sun saki matar amma suka ci gaba da tsare yaranta guda biyu.

Kara karanta wannan

Kasuwar Yobe ta gamu da iftila'I, shaguna sama da 40 sun kone kurmus

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An kama mai taimakawa 'yan bindiga

Jami'an NSCDC a jihar Kwara sun kama wani mutum mai suna Abu Usman Soja wanda ake zargin shi ne mai ba wa masu garkuwa da mutanen bayanai.

Bayan haka, an zargi Abu Usman Soja da amfani da wayarsa wajen tuntuɓar iyalan wadanda aka sace domin karbar kudin fansa.

Yaushe aka kama Abu Usman Soja?

Sahara Reporters ta wallafa cewa kwamandan NSCDC na jihar Kwara, Dr Umar Muhammed ya tabbatar da kama Soja a yau Talata, 3 ga Disamba.

Dr Umar Muhammed ya ce Soja da wasu abokan cin mushensa wadanda yanzu haka sun gudu, sun yi garkuwa da matar da ‘ya’yanta biyu a ranar 7 ga Nuwamba.

Masu garkuwa da mutane sun rage kudin fansa

Kwamandan ya kara da cewa masu garkuwan sun fara neman fansar Naira miliyan 50, amma daga baya sun rage zuwa Naira miliyan 15.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta fara cire haraji daga masu amfani da Opay, Moniepoint da sauran bankuna

Ana sa ran jami'an NSCDC za su cigaba da kokarin cafko sauran wadanda suke da hannu a garkuwar domin ceto yaran da ke hannunsu.

An sace tsohon dan majalisa a Nasarawa

A wani rahoton, kun ji cewa miyagun ƴan bindiga sun yi garkuwa da tsohon ɗan majalisar wakilan tarayya, Hon. Dr Joseph Haruna Kigbu a jihar Nasarawa.

Maharan sun buɗe wuta kan matafiya, inda suka kashe ɗan sanda ɗaya kafin daga bisani su yi awon gaba da ɗan siyasar a hanyarsa ta zuwa Jos.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng