Gwamnatin Kano Ta Shiga Damuwa, Lokaci Zai Kure An Gagara Sayen Kujerun Aikin Hajji
- Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta ce ba ta ji dadin yadda jama'a ke jan kafa wajen fara biyan kafin alkalamin aikin hajji ba
- Hukumar jin dadin alhazai ta kasa (NAHCON) ta yi umarnin a fara karbar N8.4m daga maniyyatan jihar
- Amma shugaban hukumar a Kano, Lamin Rabi'u Baffa ya ce har yanzu jama'a ba su fara sayen kujerun yadda ya dace ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta bayyana fargaba ganin yadda jama'a har yanzu, ba su fara sayen kujerar aikin hajjin 2025 ba.
Shugaban hukumar alhazai ta jihar, Lamin Rabi’u Danbappa ne ya bayyana haka a yau Talata a lokacin da ya ke ganawa da jami'an hukumar a kananan hukumomi.
BBC Hausa ta ruwaito cewa jami'in yada labaran hukumar, Suleiman A Dederi, ta cikin sanarwar da ya sa wa hannu, bukaci ma'aikatan su tashi haikan son sayar da kujerun.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Fatan gwamnatin Kano kan aikin hajji
Suleiman A Dederi ya shaidawa Legit cewa ana fatan kujerun da aka ba jihar Kano za su kare kafin a wa'adin rufe sayen kujerun aikin hajji ya cika.
Da aka tambaye shi ko tsadar kafin alkalamin kujerar aikin hajjin ne ya sa jama'a ba sa saye, ya ce;
"Ba za mu iya tantancewa ko kudin ne ya sa ba a saye ba, amma mu na fatan kujerun za su kare kafin lokacin aikin hajji."
Ya tabbatar da cewa hukumar alhazai ta kasa (NAHCON) ta yi umarnin a fara karbar N8.4m a matsayin kafin alkalin aikin hajjin 2025.
Gwamnati ya ba jami'anta umarni kan aikin hajji
Hukumar jin dadin alhazan jihar Kano ta umarci ma'aikatanta da su bullo da dabarun sayar da kujerun da aka ba kananan hukumominsu.
Hukumar alhazan ta sanya ranar 1 ga watan Janairu 2025, a matsayin ranar rufe karbar kafin alkalami daga maniyyatan jihar Kano.
Gwamnati za ta mayar wa mahajjata kudinsu
A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin jihar Jigawa na shirin mayarwa alhazan da ba su samu kulawar da ta dace yayin aikin hajjin 2023 ba wani kaso da kudin da su ka biya.
Shugaban hukumar kula da jin dadin alhazai a Jigawa, Ahmad Labbo ya ce kowane mahajjaci daga cikin mutum 1571, zai samu N61,080 daga cikin kudin da ya biya na hajjin 2023.
Asali: Legit.ng