Gwamna Ya Fadi Yadda Aka Kubutar da Kananan Yara 4 da 'Yan Bindiga Suka Sace a Kaduna

Gwamna Ya Fadi Yadda Aka Kubutar da Kananan Yara 4 da 'Yan Bindiga Suka Sace a Kaduna

  • An saki yara hudu da aka sace a Millennium City da ke Chikun sakamakon yarjejeniyar zaman lafiya ta gwamnatin Kaduna
  • Gwamna Uba Sani ya ce sun mayar da hankali wajen gina amana domin kaucewa matsala a yarjejeniyar zaman lafiyar a Kaduna
  • Gwamnatin Kaduna na fatan shirin zaman lafiyar ya zama abin koyi ga sauran jihohin Arewa maso Yamma da Arewa baki ɗaya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kaduna - Gwamnan Kaduna, Uba Sani, ya sanar da sakin yara hudu da aka sace a Millennium City da ke karamar hukumar Chikun ta jihar.

Malam Nuhu Ribadu, mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro, ya mika yaran ga Gwamna Uba Sani, kamar yadda gwamnan ya sanar.

Gwamna Uba Sani ya yi magana yayin da aka ceto yara 4 da 'yan bindiga suka sace a Kaduna
Gwamna Uba Sani ya jinjinawa Nuhu Ribadu bayan ceto yara hudu da aka sace a Kaduna. Hoto: @ubasanius
Asali: Twitter

An kubutar da yaran da aka sace a Kaduna

A wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X a ranar Talata, Uba Sani ya ce ya hada yaran da iyayensu bayan karbarsu daga hannun Nuhu Ribadu.

Kara karanta wannan

"Abin da ya kamata Tinubu ya yi kan gyaran haraji," Dan majalisar Arewa ya magantu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Legit Hausa ta rahoto cewa akwai yaro dan shekara biyu a cikin yaran da aka sace, sauran kuwa mata ne masu shekaru tara, 12 da kuma 15.

Gwamna Uba Sani ya ce samun nasarar kubutar da yaran ya biyo bayan wata yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimmawa karkashin kwamitin sulhu na gwamnatin Kaduna.

Gwamnatin Kaduna ta kafa kwamitin tattaunawar zaman lafiya da 'yan bindiga tare hadin gwiwar ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro.

Amfanin yarjejeniyar zaman lafiya a Kaduna

Gwamna Uba Sani ya ce sun yi tukuru wajen gina amana a tsakanin gwamnati da 'yan bindiga kuma matsalar rashin yarda ce ta haifar da shan wahalar yarjejeniyar.

Duk da yunkurin masu cin moriyar rikicin na hana tattaunawar zaman lafiyar ta yi nasara, gwamnatin Kaduna ta ce shirinta bai fadi kasa banza ba.

"Nasarar da aka samu a Birnin Gwari tana ƙara tasiri, kuma sakin yaran Millennium City ya tabbatar da nasarar tsarin zaman lafiya na Kaduna."

Kara karanta wannan

'Abin da ya sa ake zaune lafiya a Kano duk da matsalar tsaron Arewa maso Yamma'

- A cewar Uba Sani.

Gwamnan jihar na Kaduna ya ce irin wannan tsarin zaman lafiyar zai iya zama abin koyi ga jihohin Arewa maso Yamma, har ma zuwa dukkanin yankunan Arewa.

An nemi N300m a matsayin kudin fansa

Tun da fari, mun ruwaito cewa miyagun 'yan bindigar da suka sace kananan yara hudu a jihar Kaduna sun nemi N300m kudin fansar yaran.

Masu garkuwan sun kira mahaifin yaran tare gabatar masa da bukatarsu, kuma suka gargade shi a kan za su kashe karamin cikinsu saboda ya ishe su da kuka.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.