Peter Obi Ya Ɗan Saba da Yan Arewa kan Kudirin Haraji, Ya ba da Shawara
- Tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi ya bayyana matsayarsa kan ce-ce-ku-ce da ake yi game da sabon kudirin haraji
- Obi ya ce tabbas kudirin yana da kyau amma ya kamata a duba tasirin da zai yi ga kasar da kuma sauran yankunanta
- Tsohon dan takarar shugaban kasa a LP ya ce dole a wayar da kan al’umma da kuma jin ra’ayinsu domin sanin abin da ke ciki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja – 'Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar LP, Peter Obi ya yi magana kan sabon kudirin haraji da ake ta ka-ce-na-ce a kai.
Peter Obi ya ce yana goyon bayan kudirin harajin sai dai dole a yi duba kan tasirinsa ga kasar da yiwuwar cigaba da kasancewar yankunanta.
Peter Obi ya magantu kan kudirin haraji
Tsohon gwamnan ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X a jiya Litinin 2 ga watan Disambar 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Obi ya ce bai kamata a yi duba kawai ga bangaren da gwamnatin za ta samu riba ba wurin samar mata da haraji.
Ya ce dole a duba tasirin hakan ga Najeriya da kuma cigaban yankun kasar da kuma wayar da kan jama’a.
“Dole mu yi duba kan abin da zai shafi kasar da kuma cigaban sauran yankunanta tare da wayar da kan al’umma.”
“Aminci da kuma halastaccen tsari shi ne ginshikin samar da shugabanci nigari yayin da idan aka rasa haka za a samu matsala.”
- Peter Obi
Obi ya ba gwamnati shawara kan kudirin haraji
Peter Obi ya ce sauya tsarin haraji da ake son yi yana da matukar kyau kuma babu wata matsala game da tabbatar da ita.
Ya ce irin wadannan sauye-sauye suna bukatar jin ra’ayin jama’a saboda sanin muhimmacin kudirin wanda zai ba su damar ba da gudunmawa.
Atiku ya yi magana kan kudirin haraji
Kun ji cewa tsohon dan takarar shugaban kasa a PDP, Atiku Abubakar ya ba Majalisar Tarayya shawarwari kan kudirin haraji.
Atiku Abubakar ya bukaci sake duba abubuwan da ke cikin kudirin domin tabbatar da cewa sun dace da muradun yan Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng