Kasuwar Yobe Ta Gamu da Iftila'i, Shaguna Sama da 40 Sun Kone Kurmus
- ‘Yan kasuwar Bayan Tasha da ke Damaturu a jihar Yobe, sun wayi gari da iftila’in mummunan gobarar cikin dare
- Shaidar gani da ido ya bayyana cewa wutar na tashi da misalin 3.00 na safe jim kadan bayan an dawo da wutar lantarki
- Hukumomi su tabbatar da cewa akalla shaguna 50 ne su ka kone kurmus, yayin da aka yi kokarin shawo kan wutar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Yobe - Mummunar gobara ta tashi da sanyin Safiya, inda ta jawo gagarumar asara a babbar kasuwar Bayan Tasha da ke Damaturu, jihar Yobe.
Hukumomi sun tabbatar da cewa gobarar ta tashi da karfe 3.00 n.s bayan an dawo da wutar lantarki a yankin.
Channels Television ta cewa duk da an samu taimako daga hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa, sai da gobarar ta tafka gagarumar barna.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gobara ta kona shaguna kusan 50 a Yobe
Shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Yobe, Dr. Muhammad Goje ya tabbatarwa da Legit afkuwar gobara a kasuwar Bayan Tasha.
Dr. Goje ya ce;
"Akalla, an yi asarar shaguna kusan 46, a yayin da mu ke kididdiga yanzu. Mutane masu shaguna da masu tebura wanda abin ya shafa sun kai kusan mutum 65. A yanzu dai muna tattara bayanai na abin da aka yi asara."
Ya tabbatar da cewa ba a samu asarar rayuka, ko an samu wadanda su ka jikkata sakamakon gobarar ba.
Gobara ta yi barna a kasuwar Yobe
Rahotanni sun bayyana yadda gobarar yau Talata ta afku shekara guda cif da samun makamanciyar iftila’in da ta kone shaguna dama a kasuwar ta Bayan Tasha.
Yayin da ‘yan kasuwa ke cikin jimami, ana gani cewa wannan gobara ta shiga cikin jerin iftila’in gobara mafi muni a jihar.
Gobara ta tashi a birnin Abuja
A baya kun ji cewa an samu afkuwar mummunar gobar, wacce ta tashi da tsakar dare a rukunin gidajen Trademore, a Lugbe cikin birnin tarayya Abuja tare da jawo babbar asara.
Jami’an kashe gobara sun kai agajin gaggawa wajen gobarar da ake zargin wutar lantarki ta haddasa, inda aka rika faftukar kawo karshen kafin a samu nasarar hana ta yaduwa.
Asali: Legit.ng