Dalilin da Ya Sa har Yanzu Wasu Ma’aikatan Kwara ba Su Samu Albashin Nuwamba ba

Dalilin da Ya Sa har Yanzu Wasu Ma’aikatan Kwara ba Su Samu Albashin Nuwamba ba

  • Ma’aikatar kudi ta Kwara ta ce akwai ma’aikatan jihar da ba su samu albashi ba saboda rashin kammala rajistar KWSRRA
  • Domin tabbatar da cewa an yiwa jama'a aiki, gwamnatin jihar ta fara biyan albashi a sabon tsarin da ta aiwatar a Nuwamba
  • Gwamnatin Kwara ta yi wa wadanda ba su samu albashin Nuwamba ba bayanin matakin da za su dauka domin samun kudinsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kwara - Ma’aikatar kudi ta Kwara ta bayyana dalilin da ya sa har yanzu wasu ma’aikatan jihar ba su samu albashin watan Nuwamba ba.

Kwamishiniyar kudi, Hauwa Nuru, ta ce ma’aikatan da abin ya shafa ba su kammala rajista da hukumar KWSRRA ba.

Gwamnatin Kwara ta yi magana yayin da wasu ma'aikatan jihar ba su samun albashin Nuwamba ba
Gwamnatin jihar Kwara ta fadi dalilin da ya sa wasu ma'aikatan jihar ba su ga albashin Nuwamba ba. Hoto: @RealAARahman
Asali: Twitter

Misis Hauwa Nuru ta bukaci ma’aikatan da ba su samu albashinsu na Nuwamba ba da su ziyarci ofisoshin KWSRRA mafi kusa a cewar rahoton Premium Times.

Kara karanta wannan

Majalisa ta hango matsala a shirin CBN na sallamar mutum 1000, ta tsayawa ma'aikata

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin Kwara ta yi magana kan albashi

Kwamishiniyar ta ce tuni aka fara biyan albashin Nuwamba, kuma wasu ma’aikatan jihar a ma'aikatu daban daban sun riga da sun samu albashinsu.

Kwamishiniyar ta ce an fara biyan ma’aikatan kananan hukumomi da malaman SUBEB bayan da suka kammala rajista da hukumar KWSRRA.

Ta ce an raba biyan albashin zuwa matakai domin tabbatar da ingancin bayanan ma’aikatan a cikin tsarin biyan albashi.

Manufar bullo da tsari rajistar KWSRRA

Punch ta rahoto cewa wannan matakin yana da nufin inganta tsare-tsare, tabbatar da gaskiyar biyan albashi da kuma karfafa amana ga jama’a.

Kwamishiniyar ta ce gwamnati ta bullo da tsarin rajistar ma'aika a hukumar KWASRRA domin adana bayanan ma'aikatan da ba su lambar shaidar zama 'yan jihar.

Misis Hauwa Nuru ta ce ma’aikatan da ba su ga albashinsu ba, za su ziyarci ofisoshin KWSRRA domin su yi rajista, kuma bayan tantancewa, za a sakar masu albashinsu.

Kara karanta wannan

Gwamnan Neja ya fara biyan albashin da ya fi na sauran jihohin Arewa ta Tsakiya

Gwamna zai fara rike albashin ma'aikata

Tun da fari, mun ruwaito cewa gwamnan Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq ya bayyana cewa ba zai biya albashin Nuwamba ga ma'aikatan da ba su yi rajista da KWSRRA ba.

Gwamnatin Kwara ta bukaci dukkanin ma'aikatan jihar da su tabbatar sun yi rajista da hukumar KWSRRA domin mallakar lambar shaidar dan zama jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.