"Abin da Ya Kamata Tinubu Ya Yi kan Gyaran Haraji," Dan Majalisar Arewa Ya Magantu

"Abin da Ya Kamata Tinubu Ya Yi kan Gyaran Haraji," Dan Majalisar Arewa Ya Magantu

  • Dan majalisar tarayya mai wakiltar Damboa/Gwoza/Chibok, Hon. Ahmadu Jaha ya yi magana kan kudurin gyaran haraji
  • Hon. Ahmadu Jaha ya bukaci shugaban kasa Bola Tinubu da ya janye kudurin gyaran harajin daga zauren majalisar tarayya
  • Ya shaidawa Tinubu cewa 'Arewa ba malalata ba ne' sannan ya ba shi shawarar yadda zai bullowa masu adawa da kudurin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Dan majalisa mai wakiltar mazabar Damboa/Gwoza/Chibok a majalisar wakilai ya nemi Shugaba Bola Tinubu ya janye kudurin gyaran haraji.

Hon. Ahmadu Jaha ya ce 'yan Najeriya za su iya amincewa da kudurin gyaran harajin ne kawai idan Tinubu ya yi abin da ya kamata.

Dan majalisar wakilai daga Arewa ya yi magana kan kudurin gyaran haraji
Dan majalisa daga Arewa ya bukaci Tinubu ya janye kudurin gyaran haraji. Hoto: @giscorng, @ubasanius
Asali: Twitter

A yayin wata hira da NTA News, dan majalisar wakilan daga jihar Borno ya bukaci gwamnatin tarayya ta janye kudurin daga majalisa sanna ta yi masa garambawul.

Kara karanta wannan

'Kudirin haraji zai iya jefa Najeriya a tashin hankali,' Dattijo ya yi gargadi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Abin da muke ba gwamnati shawara shi ne, ta janye wannan kudiri daga majalisar tarayya, a yi kwaskwarima a bangarorin da aka fahimci ana adawa da su.
"Idan har kana son taimakawa jihohin Najeriya, musamman marasa karfi, to kamata ya yi ka rika raba kaso 20% na harajin kamfanoni ga inda ake amfani da kayayyakinsu."

- A cewar Hon. Ahmadu Jaha.

Dan majalisar ya nuna damuwa kan yadda shugaban kasar ya toshe kunnensa a lokutan da ake ta kiraye kiraye na janye gyaran harajin saboda yanayin tattalin kasar.

'Arewa ba malalata ba ne' - Hon. Jaha

Hon. Ahmadu Jaha ya sake tuno kalaman tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari da ya alamta matasan Najeriya da 'malalata' inda ya dan majalisar ya ce "mu ba malalata ba ne."

"Da mu malalata ne da ba mu samar da manyan mutane irinsu Aliko Dangote ba, ga Abdulsamad Isayaka Rabiu, ga irinsu Muhammad Indimi da sauransu.

Kara karanta wannan

Gyaran haraji: Kudurin da Tinubu ya gabatar zai jefa Arewa a cikin mawuyacin hali?

"Amma gwamnati ce ta sa kasuwanci ya ki ci gaba a yankin, wanda ya tilasta kamfanoni kafa hedikwatoci a wasu yankunan da ba na Arewa ba."

- A cewar dan majalisar.

Kalli bidiyon a kasa:

'Gyaran haraji ba zai lalata Arewa ba' - Onanuga

A wani labarin, mun ruwaito cewa fadar shugaban kasa ta shaidawa 'yan Arewa cewa kudurin gyaran haraji ba zai zamo barazana ga tattalin arziki ko ci gaban yankinsu ba.

Bayo Onanuga, mai magana da yawun Shugaba Bola Tinubu ya ce damuwar da ake nunawa kan gyaran haraji ba shi da tushe domin gyaran zai zamo mai amfani ga talaka.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.