'A Tafawa Barau': An Sake Yin Rubdugu kan Rarara da Ya Saki Wakar Sanatan game da Haraji
- Mawaki, Dauda Kahutu Rarara ya sake jawowa kansa suka bayan fitar da wata sabuwar wakar Sanata Barau Jibrin
- Mawakin ya fitar da sabuwar wakar a daren jiya Litinin 2 ga watan Disambar 2024 da ya jawo surutu a tsakanin al'umma
- Wannan na zuwa ne yayin da ake ta ce-ce-ku-ce kan sabon kudirin haraji da ake zargin zai cutar da Arewa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Yan Najeriya da dama musamman a Arewa sun caccaki mawaki, Dauda Kahutu Rarara.
Rarara ya sha suka ne bayan sakin sabuwar waka da ke yabon Sanata Barau Jibrin ana tsaka da ce-ce-ku-ce game da kudirin haraji.
Rarara ya sake sabuwar waka kan haraji
A cikin wakar da Rarara ya wallafa a shafin Facebook, an jiyo mawakin na yabon Sanata Barau Jibrin kan harajin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin wakar, Rarara ya yabi Barau inda ya ce a cikin kudirin haraji an soke haraji kan kayan masarufi.
Sannan ya yabawa sanatan kan cire harajin ilimi da kuma ɓangaren lafiya inda ya ke cewa a tafawa Barau.
Wakar mai taken 'A tafawa Barau' ta jawo ka-ce-na-ce inda yan Arewa da dama suka yi Allah wadai da Rarara.
Al'umma da dama sun yi korafi inda suke cewa kwata-kwata Rarara ba shi da kishin Arewa a zuciyarsa.
Martanin yan Najeriya kan wakar Rarara
Itz Khaleefah Deeneey:
"Rarara irin ku a siyasar Arewa musifa ne domin kuke mai da Arewa baya ko da yaushe."
"Sam bukatar ku ce a gabanku, ba bukatar al'umma ba to amma Alhamdulillah tun da Allah yana kallon kowa."
Real B Habu:
"Kai kuma tun da burinka kare karya da zaluncin talaka Allah ya sa ka ga abin da kake shukawa talakawan kasar nan kafin ka mutu."
Babangida Lawan Duwan:
"Idan kana neman mutum wanda bai damu da yankinsa ba sai abin da zai samu da ka samu Rarara shikenan."
"A yadda na fahimci Rarara tsaf da ace yana da dama zai siyar da garinsu a ba shi kudin ya tafi India kallon yan mata."
Barau ya fayyace yadda kudirin haraji yake
A baya, kun ji cewa Sanata Barau Jibrin ya yi ƙarin haske kan ce-ce-ku-ce da ake yi game da sabon kudirin haraji a Najeriya.
Barau ya ce mafi yawan al'umma ciki har da wasu Sanatoci ba su fahimci abin da ke kunshe a kudirin ba da ake zargin zai cutar da Arewa.
Hakan ya biyo bayan caccakar Sanata Barau da ya jagoranci zaman Majalisar Dattawa a lokaci da ake muhawara kan kudirin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng