Gyaran Haraji: Kudurin da Tinubu Ya Gabatar Zai Jefa Arewa a cikin Mawuyacin Hali?

Gyaran Haraji: Kudurin da Tinubu Ya Gabatar Zai Jefa Arewa a cikin Mawuyacin Hali?

  • Fadar shugaban kasa ta musanta cewa gyaran haraji zai amfani Legas da Ribas ne kawai, inda ta ce kudurin ba zai lalata Arewa ba
  • Bayo Onanuga ya bayyana damuwar da aka nuna kan gyaran harajin a matsayin rashin fahimta, yana mai kira ga hadin kan kasa
  • Ba za a soke hukumomin TETFUND, NASENI, da NITDA ba, za su ci gaba da aiki tare da samun kudi daga kasafi, a cewar Onanuga

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Fadar shugaban kasa ta musanta ikirarin cewa kudurin gyaran haraji zai jefa Arewacin Najeriya a mawuyacin hali ko kuma zai amfani Legas da Ribas kawai.

Bayo Onanuga, mai magana da yawun Shugaba Bola Tinubu, ya ce manufar gyaran harajin shi ne inganta rayuwar ‘yan Najeriya musamman marasa galihu.

Kara karanta wannan

"Majalisa za ta amince da kudirin haraji kuma babu abin da zai faru," Sanata

Fadar Shugaban Kasa ta martani kan ikirarin cewa gyaran haraji zai durkusar da Arewa
Fadar shugaban kasa ta ce kudurin gyaran haraji ba zai azurta Kudu ko talauta Arewa ba. Hoto: @aonanuga1956
Asali: Twitter

A cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X, Onanuga ya kara jaddada cewa babu wani bangare na harajin da zai zama barazana ga ci gaban Arewa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gyaran haraji zai gurgunta Arewa?

Legit Hausa ta rahoto cewa Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno ya nuna damuwa kan cewa tsarin raba VAT zai fi amfani ne ga jihohin Legas da Ribas.

Sai dai Onanuga ya ce akwai rashin fahimta kan yadda mutane ke nuna damuwarsu game da gyaran harajin, inda ya ce dole a natsu a fahimci gaskiyar lamari.

Fadar shugaban kasar ta ce gyaran haraji ba zai sa Legas da Ribas su fi arziki ba, kuma ba zai jefa wasu yankuna, musamman Arewa cikin talauci ba.

Amfanin gyaran haraji ga 'yan Najeriya

Onanuga ya kara da cewa, ba za a soke hukumomin TETFUND, NASENI, ko NITDA ba, suna nan suna ci gaba da aiki.

Kara karanta wannan

Kudirin haraji: Lauya ya fallasa babban burin Legas da aka kudiri niyyar tabbatarwa

Wadannan hukumomi za su ci gaba da samun kasafi ta hanyar kudaden da aka saba ware musu.

"Gyaran tsarin harajin Shugaba Tinubu zai rage wa 'yan kasuwa nauyi, tare da bunkasa cigaban kasa."
Babban dalilin Shugaba Bola Tinubu na yin garambawul ga haraji da kasafin kudi shi ne daidaita harkokin haraji da samar da yanayin gudanar da harkokin kasuwanci.

- A cewar Onanuga.

'Ba ma son gyaran haraji' - Zulum

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya shaidawa shugaba Bola Tinubu cewa Arewa ba ta son gyaran haraji.

Farfesa Zulum ya ce dokar za ta jawo koma baya ga Arewa da wasu jihohin Kudancin Najeriya don haka akwai bukatar Tinubu ya dakatar da ita.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.