ICPC: 'Yan Arewa Sun Fi Yawa cikin Wadanda Suke Gudun Cin Hanci da Rashawa

ICPC: 'Yan Arewa Sun Fi Yawa cikin Wadanda Suke Gudun Cin Hanci da Rashawa

  • Hukumar yaki da cin hanci ta ICPC ta bayyana cigaban da aka samu wurin kyamar karbar rashawa a Najeriya
  • Shugaban hukumar, Musa Aliyu shi ya tabbatar da haka inda ya ce 70% na yan Najeriya sun ki karbar cin hanci
  • Aliyu ya yabawa yankin Arewa maso Yamma a matsayin yankin da ke kan gaba wurin kyamar cin hanci a 2023

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Shugaban hukumar yaki da cin hanci ta ICPC, Musa Aliyu ya yi magana kan cigaban da hukumar ta samu a yaki da rashawa.

Musa Aliyu ya ce 70% na yan Najeriya sun ki karbar cin hanci da aka yi musu tayi a shekarar 2023.

Hukumar ICPC ta fadi nasarar da aka samu kan kyamar cin hanci a Najeriya
Shugaban hukumar ICPC, Musa Aliyu ya ce 70% sun guji karbar cin hanci a 2023. Hoto: ICPC Nigeria.
Asali: Facebook

ICPC ta fadi nasarori a yaki da cin hanci

Shugaban ICPC ya bayyana haka ne a jiya Litinin 2 ga watan Disambar 2024 a jihar Kano da shafin ICPC Nigeria ya wallafa a shafin Facebook.

Kara karanta wannan

Kazamar fada ta barke tsakanin yaran Turji da 'yan banga, manoma sun shiga yanayi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Aliyu ya ce ana samun kyamar karba ko bayar da da cin hanci a tsakanin al'umma inda 70% na yan Najeriya suka yi fatali da tayin da aka yi musu.

Ya ce hakan ya fi tasiri a yankin Arewa maso Yamma inda 76% da suka ci karo da masu ba da rashawa kuma suka ki ba su hadin kai.

Yankin da aka fi samun nasara kan cin hanci

"Cin hanci da rashawa ya zama ruwan dare a tsakanin yan Najeriya musamman ma'aikatu da bangaren tsaro da kuma wuraren haduwar jama'a."
"Duk da wadannan kalubale, abin farin ciki shi ne 70% na yan Najeriya sun ki karbar cin hanci bayan tayin da aka yi musu a 2023."
"A Arewa maso Yamma, 76% na mutane da suka ci karo da tayin rashawa sun ki amincewa wanda shi ne mafi girma tsakani sauran yankunan kasar."

- Musa Aliyu

Hukumar ICPC ta dura kan kakakin Majalisar Kano

Kara karanta wannan

'Ba a fahimci abin ba': Sanata Barau ya yi karin haske kan haraji, ya fayyace komai

Kun ji cewa Hukumar ICPC ta gayyaci kakakin majalisar Kano, Jibril Falgore da mataimakinsa, Muhammad Butu da wasu mutane uku.

An ruwaito cewa gayyatar dai wani bangare ne na binciken badakalar kwangilar magunguna ta N440m a kananan hukumomi 44 na jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.