'Yan Majalisar Arewa Sun Gana, An Dauki Matsaya kan Kudirin Harajin Tinubu

'Yan Majalisar Arewa Sun Gana, An Dauki Matsaya kan Kudirin Harajin Tinubu

  • 'Yan majalisar tarayya da su ka fito daga shiyyar Arewacin Najeriya sun fitar da matsayarsu a kan kudirin haraji
  • Guda daga cikin Sanatocin da aka tattauna da su, Buba Umaru Shehu daga jihar Bauchi ya ce ba za su amince da kudurin ba
  • Amma 'yan majalisar sun nuna alamun za su iya amincewa da kudirin idan aka cika wani sharadi mai muhimmanci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - 'Yan majalisa da su ka fito daga Arewacin Najeriya sun tattauna a kan kudirin harajin gwamnatin tarayya da ke cigaba da yamutsa hazo.

Sun bayyana cewa dukkaninsu, sun ki amincewa da kudirin harajin da Bola Tinubu da mukarrabansa ke kokarin kakabawa Najeriya.

Majalisa
'Yan majalisar Arewa sun yi watsi da kudirin harajin Tinubu Hoto: Nigerian Senate/Abbas Tajudeen
Asali: Facebook

BBC Hausa ta wallafa cewa 'yan majalisar daga jam'iyyun adawa da na APC ne su ka samu hadin kai wajen yin fatali da kudurin.

Kara karanta wannan

"Majalisa za ta amince da kudirin haraji kuma babu abin da zai faru," Sanata

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin 'yan majalisa na kin kudirin haraji

Sanata Buba Umaru Shehu daga jihar Bauchi ya bayyana dalilin da ya sa su ka bijirewa kudirin harajin gwamnatin tarayya.

Sanata Buba Umaru Shehu ya ce:

"Ba mu muka fara cewa ba mu yarda ba kudirin harajin ba, gwamnoni da sarakuna ne suka tattauna suka ga zai cutar da mu."

'Yan majalisa za su iya karbar kudirin haraji

Sanatocin Arewa sun bayyana sharadin da zai sa su amince da kudirin harajin da Bola Ahmed Tinubu ya aikawa majalisun kasar nan.

'Yan majalisar sun ce dole a cire sashen da ya ya bijiro da batun kason harajin jihohi, wanda bangaren ne ake ganin zai yi illa matuka ga Arewa.

""Idan har ba mu dauki wannan matakin ba, mu ka bari aka amince da ƙudirin, nan gaba da mu za a yi kuka."

- Sanata Buba Umaru Shehu

Lauya ya tona abin da kudirin haraji ya kunsa

Kara karanta wannan

Kudirin haraji: Lauya ya fallasa babban burin Legas da aka kudiri niyyar tabbatarwa

A wani labarin, kun ji cewa babban lauya mai fafutukar kare hakkin dan Adam, Barista Audu Bulama Bukarti ya fallasa shirin da gwamnati ta boye a kudirin haraji.

Bulama Bukarti ya ce ba tun yanzu jihar Legas ke son a kaddamar da kudirin haraji ba, ya zargi Tinubu da tattaro kan wanda za su taimaka wajen samar da dokar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.