Jarumar Fim a Najeriya Za Ta Fara Haɗa Aure, Ta Kirkiri Manhajar Haɗa Masoya

Jarumar Fim a Najeriya Za Ta Fara Haɗa Aure, Ta Kirkiri Manhajar Haɗa Masoya

  • Yawan ƴan mata a gari babu mijin aure ya jawo hankalin jarumar Nollywood, Chinonso Ukah wacce aka fi sani da Nons Miraj
  • Fitacciyar jarumar ta shirya kaddamar da sabuwar manhajar haɗa ƴan mata da samari soyayyar gaskiya da za ta kai shiga daga ciki
  • A wata sanarwa da manajar kamfanin jarumar ta fitar, ta ce an tsara manhajar daidai da zamani domin haɗa ma'aurata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Lagos - Fitacciyar jaruma a masana'antar shirya fina-finan Nollywood, Chinonso Ukah ta fara shirin fara dillancin aure don rage samari da ƴan mata.

Jarumar wacce ta shahara a kafafen sada zumunta kuma ƴar wasan barkwanci ta kirƙiro manhajar haɗa ma'aurata kuma za ta ƙaddamar da ita nan kusa.

Nons Miraj.
Jarumar Nollywood ta kirkiro manhajar haɗa ma'aurata a Najeriya Hoto: Nons Miraj
Asali: Facebook

Jarumar fim za ta fara haɗa aure

Chinonso Ukah, wanda aka fi sani da Nons Miraj za ta kaddamar da manhajar haɗa samari da ƴan mata soyayyar da za ta kai ga aure, Tribune Online ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ya kamata ku sani: Manyan abubuwa 6 masu muhimmanci da za su faru a Disambar 2024

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da manajar kamfanin Miraj Nons, Becky Joe ta rabawa manema labarai ranar Lahadi.

Joe ta bayyana cewa za a kaddamar da manhajar mai suna, 'Hunt Games dating App' ranar 4 ga watan Disamba a jihar Legas, rahoton This Day.

A cewarta, an kirkiro manhajar ne domin ba ƴan mata damar samun abokin rayuwa, wanda za su aura idan sun daidaita junansu.

Yadda aka tsara manhajar haɗa ma'aurata

Sanarwar ta ce:

"Manhajar wani dandali ne na haɗa mutane soyayya, mai tsaro da aminci babu yaudara. Za mu haɗa samari da ƴan mata da ke neman abokan rayuwa."
"Wannan sabuwar manhaja ce kuma tana da aminci, za ta taimaka maku wajen haɗuwa da masoyan gaskiya a zamanin da muke ciki na fasaha."

Becky Joe ta ƙara da cewa za a haɗa kaddamar da manhajar da wasu wasannin nishaɗi domin ƙara buɗe wata ƙofar haɗa masoya da abokan rayuwa na gaskiya.

Kara karanta wannan

Gobara ta tashi a babbar kasuwa a Abuja, ta yi barna mai yawa

Jarumin Nollywood ya ba maza shawara

A wani labarin, kun ji cewa jarumin fina-finan Nollywood da ke Kudancin Najeriya, Stephen Alajemba ya ba maza shawara kan yadda za su yi aure.

Fitaccen jarumin wanda aka fi sani da Uwaezuoke ya ce auren mata daya ko biyu babban hatsari ne kuma barazana a rayuwa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262