'Gidaje 753': EFFC Ta Kwato Babbar Kadara da ba Ta Taba Kama Irinta ba a Tarihi

'Gidaje 753': EFFC Ta Kwato Babbar Kadara da ba Ta Taba Kama Irinta ba a Tarihi

  • Alkalin kotun tarayya, Jude Onwuegbuzie ya bayar da umarnin kwace katafaren gini mai dauke da gidaje 753 a Abuja
  • An bayyana cewa ginin ne mafi girman kadara da hukumar EFCC ta kwato tun daga lokacin da aka kafa ta a shekarar 2003
  • Hukumar ta EFCC ta ce an kwace kadarar ne domin hana cin gajiyar dukiyar da aka samu ta haramtattun hanyoyi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - A yau Litinin alkalin kotun tarayya, Jude Onwuegbuzie, ya bayar da hukuncin kwace katafaren gida mai fadin mita 150,500 da ke Lokogoma a Abuja.

Rahotanni sun tabbatar da cewa wannan kwace shi ne mafi girma da hukumar EFCC ta taba yi tun da aka kafa ta.

EFCC Abuja
EFCC ta kwato kadara mafi girma. Hoto: Economic and Financial Crimes Commission
Asali: Facebook

Hukumar EFCC ta wallafa a Facebook cewa an yi amfani da kudi daga haramtattun hanyoyi wajen gina rukunin gidajen.

Kara karanta wannan

Duk da sanar da karin albashi, kungiyar NLC na nazarin shiga yajin aiki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

EFCC: Dalilin kwace babbar kadara da kotu ta yi

Yayin sauraron karar, alkalin kotun, Jude Onwuegbuzie ya ce wanda ake zargi ya gaza gabatar da kwararan dalilai da za su hana kwace kadarar da ake zargin an samu ta hanyoyi na haram.

Onwuegbuzie ya ce tun da babu wata shaida daga wanda ake tuhuma, kadarar ta zama mallakin gwamnatin tarayya.

Jaridar the Cable ta wallafa cewa hukuncin ya biyo bayan umarnin wucin gadi da kotun ta bayar a ranar 1 ga Nuwamba.

EFCC ta fadi amfanin kwace kadarar

EFCC ta bayyana cewa kwace kadarar wani bangare ne na dabarun hana masu laifi cin gajiyar abin da suka samu daga haramtattun hanyoyi

Hukumar ta kuma tabbatar da cewa ana binciken tsohon babban jami’in gwamnati da ake zargi da mallakar katafaren ginin.

Yaki da rashawa ya samu nasara inji EFCC

EFCC ta ce kwace kadarar wata gagarumar nasara ce ga hukumar a kan yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya.

Kara karanta wannan

"Mutane sun zama mabarata," Jigon APC ya koka kan tsadar kayan abinci a Najeriya

Hukumar ta bayyana cewa wannan nasara tana daga cikin alamu masu karfi na jajircewar shugaba Bola Ahmed Tinubu wajen ganin an kawar da rashawa a kasar nan.

EFCC ta gaza gurfanar da Yahaya Bello

A wani rahoton, kun ji cewa hukumar EFCC ta gaza gurfanar da tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello a kotu a ranar 28 ga Nuwamba, 2024, saboda wasu dalilai.

Yahaya Bello na fuskantar tuhume-tuhume 19 na zambar N82bn, bayan an tsare shi a wata tuhumar zambar N110.4bn da ake masa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng