Manyan Malaman Musulunci da Suka Soki Kudirin Haraji ko Goyi bayan Tsarin
Tun bayan kawo maganar sabon kudirin haraji a Najeriya, yan kasar su ke ta maganganu ciki har da malaman Musulunci.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Kudurin ya jawo maganganu daga bangarori da dama a Arewacin Najeriya cikin har da gwamnonin yankin da sarakunan gargajiya.
TABLE OF CONTENTS
Malaman Musulunci sun magantu kan kudirin haraji
Sai dai Sanata Barau Jibrin da Hon. Abdulmumin Jibrin daga Kano suna ganin rashin fahimtar abin da ke cikin kudurin ne ya sanya suke korafi da kushewa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
1. Farfesa Mansur Ibrahim Sokoto
Farfesa Mansur Sokoto ya nuna damuwa kan kudirin harajin, ya ce akwai bukatar a kammala tantance kudirin kafin a tabbatar da shi.
Sheikh Mansur Sokoto ya ce hankulan al'umma ba za su kwanta ba idan suka ga ana gaggawar tabbatar da wani kudiri, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Shehin malamin ya yi magana ne bayan majalisa ta yi karatu na biyu ga kudirin haraji duk da surutun da ake ta yi a kansa.
2. Sheikh Abubakar Salihu Zaria
Sheikh Alkali Salihu Zaria ya nuna bacin rai kan sabon kudirin haraji inda ya ce bala'in da ke cikin kudirin sai ya fi na cire tallafin mai matsala.
Malamin ya fadi haka a wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafinsa na TikTok, ya caccaki Sanata Barau Jibrin.
Sheikh Salihu Zaria ya nuna damuwa kan halin da ake ciki inda ya kira sunan wasu 'yan siyasa ya yi musu addu'o'in bala'i yayin da ya yabawa Sanata Ali Ndume.
3. Sheikh Isa Ali Pantami
A bangarensa, Sheikh Isa Ali Pantami ya yi kira ga Majalisar Tarayya da ta dakatar da kudirin dokar gyaran haraji domin sake nazari mai zurfi.
A cikin wata sanarwa a shafinsa na Facebook, tsohon ministan tarayyar ya ce akwai wasu sassa a cikin kudirin da suke bukatar sake nazari da shawara daga masu ruwa da tsaki.
Farfesa Pantami ya yi nuni da mahimmancin samun amincewa daga dukkanin masu ruwa da tsaki tare da fifita muradun ƙasa a lamarin.
4. Farfesa Ahmad Bello Dogarawa
Farfesan Ahmad Bello Dogarawa ya yi magana a cikin faifan bidiyo da shafin Islamic Trust of Nigeria ya wallafa a Facebook, ya ce masana sun yi korafi game da abubuwan cutarwa ga Arewa da ke cikin kudirin.
Malamin ya ce daga cikin kudurorin akwai masu hatsari guda biyu wadanda suka hada da haraji kan kayan masarufi da za a kara harajin VAT zuwa 10% a 2025 da kuma 15% a 2030.
"Abu na biyu shi ne kason raba haraji ga jihohi wanda za a raba 50% ga jihohi daidai sai 30% ga wadanda suka fi yawan jama'a."
"Inda ake da matsalar ita ce 20% da za a raba duba da jihar da tafi tara haraji da kuma inda aka sayi kayan, misali ka yi waya kamfanin MTN sun dauki VAT to zai wuce Lagos ne da hedikwata take."
- Farfesa Ahmad Bello Dogarawa
Haraji: Malaman da suka bambanta da saura
1. Sheikh Musa Yusuf Assadus Sunnah
Sai dai Sheikh Assadus Sunnah shi ma ya dan bambanta da sauran masu kushe lamarin sabon kuditin haraji da ake magana a kai.
A faifan bidiyo da hadimin Sanata Barau Jibrin mai suna Dan Kuda Kabo ya wallafa a shafin Facebook, malamin ya ce ya kamata a tsaya a fahimci kudirin kafin malamai su yi magana.
Shehi ya ce karanto doka daban haka goyon bayanta daban, ya kamata a yi adalci domin ka da a yi ta hauragiya kan abin da kawai ake yayatawa.
Ya ce ya kamata al'umma ta zama masu adalci saboda akwai sanatoci 109 amma da dama ba a ji sun yi magana kan kudirin ba, dole a san su waye suka goyi baya ko sabanin haka.
2. Sheikh Ahmad Mahmud Gumi
A bangarensa, shehin malamin ya yi hannun-riga da sauran malamai, ya goyi bayan sabon kudirin haraji da ake ta magana a kai.
Sheikh Ahmad Gumi yayin nuna goyon bayansa ga ƙudirin, ya bayyana cewa dokokin suna da amfani a Najeriya.
Shehin malamin ya bayyana haka a wani bidiyo a shafinsa na Facebook, yake cewa daga cikin masu sukar ƙudirin, ba su fahimci abin da kundin da aka kai Majalisa ya ƙunsa ba.
Sanata Barau ya fayyace sabon kudirin haraji
A baya, kun ji cewa duk da hayaniyar da ake ta yi kan kudirin haraji da Majalisar Tarayya ta yi zama a kai, Sanata Barau Jibrin ya yi karin haske.
Mataimakin shugaban Majalisar ya fayyace yadda lamarin yadda kudirin haraji yake inda ya ce ba a yi komai ba yanzu ma aka fara muhawara a kai.
Asali: Legit.ng