Shugaban Majalisa Ya Gano Matsalolin da Suka Hana Kananan Hukumomi Ci Gaba

Shugaban Majalisa Ya Gano Matsalolin da Suka Hana Kananan Hukumomi Ci Gaba

  • Shugaban majalisar wakilan Najeriya, Abbas Tajudeen, ya koka kan matsalolin da suka hana ƙananan hukumomi samun ci gaba
  • Abbas Tajudeen ya bayyana cewa ƙalubalen rashin ƴancin cin gashin kai, cin hanci da rashawa suna kawo cikas ga ƙananan hukumomi
  • Ya nuna cewa lokaci ya yi da za a kawo ƙarshen hakan domin ƙananan hukumomin su tsaya da ƙafafunsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaban majalisar wakilai, Tajudeen Abbas, ya yi magana kan matsalolin da ke addabar ƙananan hukumomi a Najeriya.

Shugaban majalisar ya bayyana cewa rashin ƴancin cin gashin kai, cin hanci da rashawa, rashin isassun kuɗaɗe, da sauransu na haifar da gagarumin cikas ga ayyukan ƙananan hukumomi.

Abbas Tajudeen ya tabo matsalolin kananan hukumomi
Abbas Tajudeen ya koka kan matsalolin kananan hukumomi Hoto: Hon. Tajudeen Abbas
Asali: Facebook

Ya bayyana hakan ne a jawabinsa na buɗe taro kan 'ƙananan hukumomi da kundin tsarin mulki' wanda aka gudanar a Abuja ranar Litinin, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Kudirin haraji: Kungiya ta shirya azumi domin Zulum da Ndume, ta fadi dalili

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me shugaban majalisa ya ce kan ƙananan hukumomi?

Tajudeen Abbas ya nuna cewa ƙananan hukumomi na taka muhimmiyar rawa wajen samar da ayyuka, da inganta ci gaban al’umma.

"Abin bakin ciki, duk da kyakkyawan ƙudiri da masu rubuta kundin tsarin mulkin mu suke da shi na kafa tsarin ƙananan hukumomi, a bayyane yake cewa akwai manyan kalubale da ke kawo musu cikas."
"Abubuwan da suka haɗa da rashin isassun kuɗaɗe, rashin ƴancin cin gashin kai, rashin isashen iko, cin hanci da rashawa, da dai sauransu, sun hana ƙananan hukumomi yin kataɓus tsawom shekaru da dama."

"Waɗannan ƙalubalen ba wai kawai su na kawo cikas ga gudanar da mulki ba ne, har ma suna kawo naƙasu ga ci gaban ƙasa. Akwai buƙatar a gyara hakan."

- Tajudeen Abbas

Jigon APC ya caccaki Abbas Tajudeen

A wani labarin kuma, kun ji cewa naɗa hadimai 600 da shugaban majalisar wakilai, Hon. Tajudeen Abbas ya yi ya jawo ce-ce-ku-ce a cikin jam'iyyar APC musamman bayan maganar Taslim Dan-Wanki.

Jigon APC, Taslim Dan-Wanki ya caccaki kakakin majalisar kan wadannan nade nade da ya yi inda har ya ke kalubalantar nagartarsa a siyasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng