Duk da Sanar da Karin Albashi, Kungiyar NLC Na Nazarin Shiga Yajin Aiki
- Yayin da 'yan kwadago ke tsaka da shirin shiga yajin aiki, gwamnatin Cross River ta sanar da mafi karancin albashi
- Gwamnati da 'yan kwadago sun cimma yarjejeniya kan sabon albashi bayan tarukan da suka rika yi tun ranar Alhamis
- Shugaban TUC na jihar ya tabbatar da yarjejeniya tare da cewa za su gudanar da taron kungiyar kwadago a gaba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Cross River - Gwamnatin jihar Cross River ta amince da sabon mafi karancin albashi na N70,000 ga ma’aikatan gwamnatin jihar.
Rahotanni na nuni da cewa gwamnatin za ta fara aiwatar da karin kudin ne daga ranar 1 ga watan Disambar 2024.
Jaridar the Nation ta wallafa cewa shugabannin kwadago a jihar Cross River sun tabbatar da samun sanarwar karin albashin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan Kwadago da karin albashi a Cross River
Rahoton TVC ya nuna cewa shugaban kungiyar TUC na jihar, Monday Ogbodum, ya tabbatar da yarjejeniyar da suka cimma da gwamnati kan karin albashi,.
Sai dai duk da haka, Monday Ogbodum ya bayyana cewa za su gudanar da taron kungiyar kwadago domin daukar mataki na gaba.
“Mun cimma yarjejeniya da sanya hannu kan aiwatar da sabon mafi karancin albashi tare da karin albashi a dukkan matakai. An yi haka ne bisa la’akari da yanayin tattalin jihar."
- Monday Ogbodum. shugaban TUC
Cross River za ta shiga yajin aiki?
Kungiyar NLC za ta fara yajin aiki a ranar yau Litinin domin neman aiwatar da dokar mafi karancin albashi ta shekarar 2024 a wasu jihohi.
Cross River na cikin jihohin da yan kwadago suka yi barazanar tafiya yajin aiki kafin gwamnatin jihar ta sanar da karin albashi.
Dangane da matsayarsu a kan yajin aikin, Monday Ogbodum ya ce za su tattauna a yau Litinin kafin yanke shawarar karshe.
Radda ya yi karin albashi a Katsina
A wani rahoton kun ji cewa gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Radda ya sanar da amincewa da sabon mafi ƙarancin albashi ga ma'aikata.
Dikko Umaru Radda ya amince da N70,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi ga ma'aikatan jihar bayan an kammala tattaunawa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng