Rundunar 'Yan Sanda Ta Yi Martani kan Rahoton Kisan Masu Zanga Zanga
- 'Yan sandan kasar nan sun fusata bisa rahoton da kungiyar kare hakkin dan Adam, Amnesty Int'l ta fitar a kwanan nan
- Kungiyar da ke fafutukar kare hakkin bil Adama ta zargi 'yan sandan da kisan mutane 24 a lokutan zanga zangar kwana 10
- A martaninta, rundunar ta ce jami'anta sun yi aiki a doron dokar kare mutuncin jama'a a lokutan nuna adawa da gwamnati
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Rundunar 'yan Sandan kasar nan ce akwai alamar tambaya a kan rahoton Amnesty Int’l na kisan wadansu daga cikin masu zanga-zanga.
Wannan na zuwa ne bayan kungiyar kare hakkin dan Adam ta duniya ta fitar da rahoto mai shafi 34 na a kan zanga-zangar da aka yi a Najeriya.
A sakon da rundunar ‘yan sandan ta wallafa a shafinta na X, ta ce akwai kura-kurai a cikin rahoton da kungiyar ta fitar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan sanda sun musanta kashe ‘yan zanga zanga
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa rundunar ‘yan sandan kasar nan ta ce jami’anta ba su kashe masu zanga-zangar adawa da yunwa a kasar nan ba.
Sanarwar da rundunar ta fitar ta ce;
“Rundunar ta karyata waɗannan zarge-zarge ba ki daya, kuma marasa marasa tushe.”
Jami'an 'yan sanda sun kare hakkin dan Adam
Sufeto Janar na rundunar ‘yan sandan kasar nan ta ce jami’anta sun bi dokokin aiki da kare hakkin dan Adam a lokacin zanga-zangar kwanaki 10.
Rundunar ta bayyana cewa an dauki wasu bayanai ba dai-dai ba, kamar lokacin da harin ‘yan Boko Haram ya kashe mutane da dama, amma aka ce yan sanda ne.
Zanga Zanga: Za a binciki ayyukan 'yan sanda
Rundunar 'yan sandan kasar nan ta bayar da umarnin gudanar da bincike kan rahoton Amnesty Int'l da ke ikirarin cewa an kashe wasu daga cikin masu zanga-zanga.
Rundunar ta jaddada matsayarta na kare hakkin al'umma tare da bin dokokin da aka gindaya wajen tabbatar da bin doka da aiki bisa tsarin da aka tanada.
'Yan sanda sun shirya tunkarar zanga zanga
A baya, mun ruwaito cewa rundunar 'yan sandan kasar nan ta bayyana irin shirin da ta ke yi wajen tunkarar masu zanga zangar adawa da manufofin shugaban kasa, Bola Tinubu.
A cewar rundunar, an yi shirin tabbatar da tsaro, yayin da jama'a ke fitowa tituna domin nuna fushinsu kan yadda yunwa da rashin abin hannu ya yi katutu a cikin al'umma.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng