Kudirin Haraji: Kungiya Ta Shirya Azumi Domin Zulum da Ndume, Ta Fadi Dalili

Kudirin Haraji: Kungiya Ta Shirya Azumi Domin Zulum da Ndume, Ta Fadi Dalili

  • Ƙungiyar SBCC ta nuna jin daɗinta kan yadda Gwamna Babagana Umara Zulum da Sanata Ali Ndume ke adawa da ƙudirin haraji
  • Bisa hakan ne ƙungiyar ta shirya gudanar da azumi domin karrama shugabannin biyu waɗanda suka fito daga jihar Borrno
  • Ƙungiyar ta buƙaci mambobinta da ke cikin gida Najeriya da ƙasashen waje da su gudanar da azumin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Borno - Ƙungiyar Southern Borno Concerned Citizens (SBCCs), ta shirya gudanar da azumi domin karramawa da nuna goyon baya ga Gwamna Babagana Zulum da Sanata Ali Ndume.

Ƙungiyar ta yi kira ga mambobinta a fadin ƙananan hukumomi tara da waɗanda ke zaune a ƙasashen waje da su gudanar da azumin na rana ɗaya.

Kungiya ta shirya azumi saboda Zulum, Ndume
Kungiyar SBCC ta shirya azumi saboda Zulum da Ndume Hoto: Professor Babagana Umara Zulum, Senator Mohammed Ali Ndume
Asali: Facebook

Shugaba kuma kakakin ƙungiyar SBCC, Kwamared Bulama Sawa, ya sanar da cewa za a gudanar da azumin ne a ranar Litinin 2 ga watan Disamban 2024, cewar rahoton jaridar Vanguard.

Kara karanta wannan

Zulum ya gargadi Tinubu, ya fadi abin da zai faru idan ya zartar da kudirin haraji

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Za a yi azumi saboda Zulum da Ndume

Ya ce hakan ya nuna matuƙar godiyar ƙungiyar ga shugabannin na Borno guda da suka tsaya tsayin daka wajen yin adawa da batun sake fasalin haraji, rahoton Independent ya tabbatar.

"Bayan tattaunawa mai zurfi da malamai da martani kan ƙudirin haraji da ke gaban majalisa, ƙungiyar SBCC ta ayyana azumin kwana ɗaya da addu’a, domin karrama Gwamna Babagana Umara Zulum da Sanata Mohammed Ali Ndume."
"Wannan azumin zai gudana ne a ranar Litinin, 2 ga watan Disamba, 2024, kuma ana kira ga dukkan ƙungiyoyin addini a Biu, Hawul, Shani, Bayo, Askira-Uba, Gwoza, Kwaya Kusar, da Damboa, da kuma waɗanda ke zaune a ƙasashe waje su yi."

- Kwamared Bulama Sawa

Bulama Sawa ya jaddada cewa azumin wata hanya ce ta nuna godiya ga Gwamna Zulum da Sanata Ndume kan yadda suke ba da kariya ga jama'a kan ƙudirin harajin.

Kara karanta wannan

Zulum ya fadi dalilin gwamnonin Arewa na son dakatar da kudirin haraji

Zulum zai samar da tashar jirgin ƙasa

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya fara ƙoƙarin kafa tarihi wajen samar da jirgin ƙasa na zamani.

Kwamishinan sufuri da makamashi na jihar Borno ya bayyana cewa ana gudanar da bincike da shawarwari domin tabbatar da nasarar aikin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng