"Ba Kin Kudurin Harajin Tinubu Na ke ba," Tsohon Hadimin Ganduje Ya Shawarci Arewa
- Tsohon dan takarar gwamnan Kano, Salihu Tanko Yakasai ya shawarci kungiyar gwamnonin Arewa kan kudurin haraji
- Ya bayar da shawarar ne bayan ya amince da matsayar da 'yan majalisar Kano su ka cimma na dakatar da duba kudurin
- A tattaunawarsa da Legit, ya ce nauyi ya rataya a wuyan manyan Arewa, don gano ta inda kudurin zai cutar da jama'a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Tsohon dan takarar gwamna a inuwa PRP a Kano, Salihu Tanko Yakasai ya bayyana matsayarsa a kan kudurin harajin gwamnatin Najeriya.
Matsayarsa na zuwa ne bayan wasu daga cikin 'yan majalisar tarayya na Kano sun bayyana cewa ba za su amince da marawa kudurin baya ba.
A sakon da ya wallafa a shafinsa na X, Salihu Tanko Yakasai ya amince da sakon da Hassan Sani Tukur, hadimin gwamna Abba Kabir Yusuf kan kafafen yada labaran zamani ya rubuta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kudirin haraji: Matsayar hadimin Ganduje
A zantawarsa da Legit, hadimin tsohon gwamnan Kano, Salihu Tanko Yakasai ya bayyana cewa ba wai ya na adawa da baki daya kudurin harajin Bola Tinubu ba ne.
Ya ce akwai bukatar manyan Arewa su saka masana a gaba domin a fitar da illoli da fa'idar da kudurin harajin ya kunsa.
Salihu Tanko Yakasai ya ce;
"A tsaya a tsefe abin. Kusan 90% na kudurin kamar yadda na gani, mutane ba su da matsala da shi.
Inda ake da matsala 'yan wurare ne kadan. Saboda da haka, na farko su Arewa, musamman kungiyar gwamnonin Arewa da kungiyar ACF da kungiyar Majalisar malamai, su fitar da matsayarsu."
"Dalilin goyon bayan 'yan majalisa," Yakasai
Salihu Tanko Yakasai ya bayyana dalilinsa na goyon bayan matsayar da 'yan majalisar Kano su ka cimma, bayan tattaunawarsu da gwamna Abba Kabir Yusuf.
"Matsyarsu ('yan majalisar Kano), shi ne a dakatar da zartar da wannan doka, har sai an yi nazari.
"Ai ba laifi a cikin a tsaya a karanci abin, masananmu su fito su ce mana ga fa'idarsa ko akasinsa."
Tsohon dan takarar gwamnan ya ce matukar aka gano illolin da ke cikin kudurin, majalisa ta yi masa kwaskwarima yadda zai dace da cigaban tattalin arzikin Arewa.
Gwamnati ta fadi amfanin kudurin haraji
A baya, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta bukaci masu adawa da sabon kudurin harajin Tinubu da su nazarci abin da ya kunsa, tare da fahimtarsa kafin su zafafa kiraye-kirayen fatali da shi.
Hadimin shugaban kasa a kan kafafen yada labarai, Sunday Dare ne ya bayar da shawarar, inda ya jaddada cewa kudurin harajin na tattare da tarin alfanu ga baki daya kasar nan.
Asali: Legit.ng