"Abubuwa 3 da Ya Dace Ƴan Majalisa Su Gyara a Kudirin Harajin Tinubu," Farfesa Ɗandago

"Abubuwa 3 da Ya Dace Ƴan Majalisa Su Gyara a Kudirin Harajin Tinubu," Farfesa Ɗandago

Gwamnatin tarayya ta nuna karara cewa ba za ta amince da janye kudirin harajin da ta gabatar a gaban majalisun kasar nan domin neman sahalewarsu ba.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Akwai alamun ƴan majalisa, kamar shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio da mataimakinsa, Barau I Jibrin na gaba-gaba a cikin masu goyon bayan kudirin.

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya umarci ma'aikatar shari'a ta hada kai da ƴan majalisa wajen gano wuraren da Arewa ke adawa da su.

An dauki matakin ne don a sauya ko a yi kwaskwarima ga wasu sassan kafin a dawo da kudurin gaban majalisa.

Dandago
Farfesa Ɗandago ya shawarci masu ruwa da tsaki kan gyaran kudirin harajin Tinubu Hoto: Umar Isa Ɗandago/Bola Tinubu
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Legit ta tattauna da tsohon kwamishinan kuɗi na Kano, kuma ƙwararre a fannin haraji, Farfesa Kabiru Isa Ɗandago, wanda ya lissafo wasu daga cikin sassan da ya dace ƴan majalisa su lura da su.

Kara karanta wannan

"Ka da ku zauna a duhu," Gwamna ya buƙaci yan Najeriya su karanta kudirin haraji

1. "A duba harajin VAT," Farfesa Ɗandago

Tsohon kwamishinan kuɗi na Kano, Farfesa Kabiru Isa Ɗandago ya ce karin harajin sayayya (VAT) da gwamnati ta ƙullo a ƙudirin haraji ya na buƙatar gyara.

Farfesa Ɗandago ya ce;

"Ya kamata a duba abubuwa guda biyu a nan, na farko dai, waɗannan ƙare-ƙare da aka ce za a rika yi, na abin da za a riƙa karba daga 7.5% zuwa 10% zuwa 12%, har zuwa 15%."
"Ƙarin irin waɗannan kuɗaɗe, ya na tunzura jama'a sosai, saboda za su shiga cikin tashin hankali na hauhawar farashin kayayyaki da hidimomi."
"Mutane wasu su na yin kuskure a kan cewa ai iya waɗanda (kaya) aka ce akwai VAT a kansu, su ne za su samu ƙarin farashi. Ba haka ba ne."

Ya bayyana cewa matuƙar aka yi wannan ƙari na VAT, zai shafi duk wani kaya da ya ke kasuwa, ko akwai VAT a kansa ko babu.

Kara karanta wannan

Kudirin haraji ya kawo sabani a majalisa, Barau da Akpabio sun saba

2. Rabon kudin harajin VAT

Ƙwararre a ɓangaren ilimin haraji kuma malami a jami'ar BUK, Farfesa Kabiru Isa Ɗandago ya nemi bayyana kalmar 'derivation' da aka yi amfani da ita a wajen raba kudin harajin VAT da za a tattaro daga jihohin ƙasar nan.

Tsohon kwamishinan ya ce;

"To yanzu kukan da ake yi shi ne kar a kai ga wannan kalmar nan da ake cewa 'derivation' ta tafi haka babu fassara."
"Idan ba a fassara ta ba, to sai a ce ai wannan dama ta na aiki, wannan fassara ce mutane za su ɗauka a zuciyarsu."
"A wannan za a ga cewa idan aka ce za a raba kuɗin a kan wannan tsarin, to wasu ƴan tsirarun jihohi ne, musamman jihar Legas za su amfana sosai da wannan kuɗin, domin an ɗaga kuɗin bisa ga doron tara kuɗin daga 20% zuwa 60%."

Ya kara da cewa raguwar jihohi, musamman na Arewa, babu ta inda za su amfana da wannan abu duk da cewa mafi yawan sayayya daga wajensu ake yi.

Kara karanta wannan

Gwamnan Legas ya yi magana kan kudirin harajin Tinubu, ya maida martani ga Zulum

3. "A waiwayi batun harajin gado," Farfesa Ɗandago

Farfesa Kabiru Isa Ɗandago, wanda ya fara rubutu a kan harajin kayan gado da ya ce ya gano a nannaɗe a cikin ƙudirin harajin, ya ce wannan ɓangare na buƙatar duba na tsanaki.

Jama'a da dama kamar Abdulqadir Wali sun wallafa rubutun Farfesa Ɗandago a shafin Facebook, inda ya yi bayanin harajin gado.

Farfesa Ɗandago ya ce;

"Waɗannan kalmomin da aka sa (dangane da harajin gado), ko dai a cire gaba ɗaya ko kuma a daɗa fassara a kansu, me ake nufi da 'family income' idan ba maganar kayan gado ba."

Ya bayyana cewa waɗannan batutuwa su na daga cikin manyan abubuwan da ya dace a tabbata an gyara a ƙudirin harajin kafin a mayar da su ga majalisar dokoki.

An shawarci gwamnoni a kan ƙudirin haraji

A baya mun ruwaito cewa tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Adamu Garba ya shawarci gwamnonin Arewa a kan su yi ƙoƙarin samar da ingantaccen ci gaba a shiyyarsu.

Kara karanta wannan

NPower: Majalisar Tarayya ta ba Tinubu sa'o'i 72 ya buɗe asusun hukumar NSIPA

Ya bayar da shawarar ne saboda a cewarsu, ƙudirin harajin Tinubu ya fito da rashin cigaba da yankin ke fama da shi, inda ya buƙaci a rungumi harkar noma da masana'antu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.