Dakarun Sojoji Sun Ragargaji 'Yan Ta'adda a Zamfara, Sun Hallaka Masu Yawa

Dakarun Sojoji Sun Ragargaji 'Yan Ta'adda a Zamfara, Sun Hallaka Masu Yawa

  • Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasara kan ƴan ta'adda masu tayar da ƙayar baya a jihar Zamfara
  • Sojojin sun hallaka ƴan ta'adda masu bayan sun yi yunƙurin kai hari a ƙaramar hukumar Maru ta jihar
  • Jami'an tsaron sun yi artabu da ƴan ta'addan ne bayan sun samu kiran gaggawa kan shirinsu na kai hari a cikin wani ƙauye

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Dakarun sojojin Najeriya na rundunar Operation Fansan Yamma, sun hallaka ƴan ta'adda masu yawa a jihar Zamfara.

Dakarun sojojin sun hallaka ƴan ta'addan ne bayan sun samu kiran gaggawa daga wajen jama'a da ƴan banga da ke ƙauyen Yar Galadima na ƙaramar hukumar Maru ta jihar Zamfara.

Sojoji sun hallaka 'yan ta'adda a Zamfara
Dakarun sojoji sun kashe 'yan ta'adda masu yawa a Zamfara Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

Hakan na ƙunshe a cikin sanarwar da kakakin rundunar, Laftanal Kanal Abubakar Abdullahi ya fitar, cewar rahoton tashar Channels tv.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun hallaka 'yan ta'adda 135, sun kubutar da mutane masu yawa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda sojoji suka ragargaji ƴan ta'adda

Ya bayyana cewa lamarin ya auku ne a ranar, 1 ga watan Disamba, lokacin da aka sanar da sojojin cewa ƴan ta'adda sun kai hari a ƙauyen da misalin ƙarfe 5:00 na safe, rahoton Leadership ya tabbatar.

“Sojojin sun mayar da martani cikin gaggawa domin kai agaji da dawo da zaman lafiya a yankin."
"A yayin sintirin, sojojin sun ci karo da ƴan ta’adda da suka yi kwanton bauna a wurare daban-daban guda biyu a kan hanyar zuwa ƙauyen."
"Sojojin sun yi nasarar wargaza kwanton ɓaunan, suka kashe ƴan ta'adda masu yawa yayin da wasu suka arce."
"Bugu da ƙari, sojojin sama na Operation Fansan Yamma sun aika jiragen sama, domin ba da taimako ga dakarun yayin da suke ci gaba da tafiya zuwa ƙauyen, inda suka ƙara kashe ƴan ta'adda da dama."

- Laftanal Kanal Abubakar Abdullahi

Ƴan bindiga sun dasa bam a Zamfara

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun sheke 'yan ta'addan Boko Haram, sun kwato makamai

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan bindiga sun dasa bam a wata gada a ƙaramar hukumar Maru, jihar Zamfara, wanda ya fashe a ranar Lahadi, 1 ga Disamban 2024.

Yan bindiga sun dasa bam din ne a kan wata gada kusa da hanyar zuwa Dansadau domin hana sojoji motsawa su kawo ɗauki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng