Gwamnati Ta Fara Cire Haraji daga Masu Amfani da Opay, Moniepoint da Sauran Bankuna

Gwamnati Ta Fara Cire Haraji daga Masu Amfani da Opay, Moniepoint da Sauran Bankuna

  • Gwamnatin tarayya ta fara cin N50 kan duk wani kudi da aka turawa masu amfani da bankunan intanet da ya haura N10,000
  • Tuni dai bankunan intanet irinsu Opay da Moniepoint suka bayyana cewa sun fara cajar kudin kuma za su tura su kai tsaye ga FIRS
  • Wasu masu sana'ar POS da 'yan kasuwa da muka zanta da su, sun nemi gwamnati da ta janye wannan haraji da iya tsanantawa talaka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Gwamnatin tarayya ta fara cire harajin N50 kan duk wata mu'amalar kudi da ta kai N10,000 daga masu amfani da bankunan intanet.

An sanar da sanya wannan haraji na Electronic Money Transfer Levy (EMTL) da ke a karkashin dokar kudi ta 2020, a ranar 9 ga Satumbar 2024.

Kara karanta wannan

'Yan majalisar Kano sun ajiye bambancin NNPP da APC a kan kudirin haraji

Gwamnatin tarayya ta fara cajar N50 ga masu amfani da bankunan intanet
An nemi Tinubu ya janye harajin N50 ga masu kananan sana'o'i. Hoto: @PBATMediaCentre
Asali: Facebook

Harajin ya shafi bankunan yanar gizo

Rahoton Tribune Online ya ce gwamnati za ta rika cire N50 daga N10,000 ko sama da hakan da aka turawa masu amfani da bankunan irinsu Opay, Moniepoint.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiyoyi da dama sun nuna rashin amincewa da wannan haraji, ciki har da kungiyar dalibai ta kasa, inda suka yi kira ga gwamnatin da ta janye shi.

Kamfanin Opay ya sanar da abokan kasuwancinsa cewa wannan haraji na FIRS ne kuma ba su cin moriyarsa a kowanne fanni.

An fara cirewa 'yan Najeriya harajin N50

Daga ranar 1 ga Disambar 2024, aka fara cire N50 daga kowane asusu da aka tura wa kudin da suka kai ko suka haura N10,000.

Sanarwar ta tabbatar da cewa wannan haraji na gwamnatin tarayya ne kuma babu wani bankin intanet da zai amfana da shi.

Kamfanin Moniepoint da Opay ma sun sanar da cewa sun fara cire wannan haraji na EMTL, inda za su mika kudin ga hukumar FIRS kai tsaye.

Kara karanta wannan

Mafi karancin albashi: An gano abin da zai iya hana NLC shiga yajin aiki a Disamba

'Yan Najeriya sun koka da harajin EMTL

Majiyarmu ta tabbatar da cewa an fara cire N50 kan duk wata mu'amala ta sama da N10,000, daga ranar 1 ga Disamba 2024.

Al'ameen Muhammad, mai sana'ar POS a Makarfi Road a Rigasan jihar Kaduna ya ce wannan harajin ya fi shafar masu sana'arsu domin cajin N50 zai jawo a karawa abokan hulda kudi.

Al'ameen ya ce:

"Dama can bankunan suna cajar mu kudi a duk lokacin da muka saka ko muka cire kudi, yanzu da aka fara cire wannan harajin, dole mu kara cajis din da muke karba.
"Ba mu samun tsabar kudi yanzu da sauki saboda karshen shekara ta zo, ka ga dole mu koma karbar sama da N200 kan kowacce N10,000."

Shugaban kamfanin MIB Stores, da ke Bakin Ruwa, Rigasa Kaduna, ya ce harajin N50 da aka fara caja ba karamar matsala ba ce ga masu kananan kasuwanci.

Kara karanta wannan

CBN ya shirya share hawayen ƴan Najeriya, ya taso bankuna kan takardun Naira

Mai kamfanin ya ce mafi akasarin abokan cinikinsu sun koma tura masu kudi ta banki, kuma bankunan intanet ne suka fi saurin karbar kudi, don haka harajin zai shafe su sosai.

Ya yi kira ga gwamnati da ta janye harajin ga 'yan kasuwar da ba sa iya hada hadar N5,000,000 a shekara, domin su ne kullum ke fama da matsin rayuwa.

Harajin da CBN ya amince bankuna su cire

A wani labari, mun ruwaito cewa babban bankin Najeriya (CBN) ya amincewa dukkanin bankunan kasar nan su cire wasu nau'ikan haraji daga abokan huldarsu.

Daga cikin harajin da bankuna ke cirewa daga asusun abokan huldarsu akwai harajin tsaron yanar gizo, harajin tura kudi, harajin buga hatimi da wasu biyu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.