Bidiyo: Yadda Ƴan Bindiga Suka Dasa Bam a Zamfara da Muguwar Ɓarnar da Ya Yi

Bidiyo: Yadda Ƴan Bindiga Suka Dasa Bam a Zamfara da Muguwar Ɓarnar da Ya Yi

  • Bam din da ‘yan bindiga suka dasa a kan wata gada a Maru ya yi sanadin mutuwar mutum guda a ranar Lahadi, 1 ga Disamba
  • Rahoto ya ce an kai harin ne domin ramuwar gayya bayan kashe jagoran ‘yan bindiga, Sani Black, a watan Satumba da ya gabata
  • Wani bidiyo ya nuna barnar da bam din ya yi yayin da aka rahoto cewa mutanen yankin Dansadau da kewaye na cikin fargaba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Zamfara - Yan bindiga sun dasa bam a wata gada a karamar hukumar Maru, jihar Zamfara, wanda ya fashe a ranar Lahadi, 1 ga Disambar 2024.

Wani mutum ya rasa ransa yayin da bam din ya fashe, inda al’amarin ya jefa jama’a cikin firgici.

Mazauna Zamfara sun yi magana yayin da bam ya tashi a yankin Dansadau
Bam ya tashi a zamfara inda ya kashe mutum 1 da kona mota kurmus. Hoto: Legit.ng
Asali: Original

'Yan bindiga sun dasa bam a jihar Zamfara

Kara karanta wannan

Yan ta'adda sun je daukar fansar kashe abokin Sububu, an hallaka su

Mazauna yankin sun ce ‘yan bindigar sun dasa bam din ne lokacin da suka je kai hari Unguwar Galadima, kamar yadda Premium Times ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Legit Hausa ta rahoto cewa, 'yan banga sun kashe ‘yan bindiga da dama yayin da suka yi yunkurin kai hari a Unguwar Galadima.

Mazauna yankin sun ce harin na ramuwar gayya ne saboda kashe shugabansu, Sani Black da jami'an tsaron sa-kai suka yi.

Tasirin Sani Black wajen ta'addancin Zamfara

An ce Sani Black ya zama shugaban ‘yan bindiga bayan rasuwar tsohon jagoransu Tsoho Buhari a watan Satumba.

Har ila yau, Sani Black ya kasance na hannun damar Halilu Sububu wanda aka kashe a wani hari ranar 13 ga Satumba.

‘Yan bindiga masu biyayya ga Sani Black ne suka kai harin amma sun jefar da makamai sun ranta a na kare bayan ganin irin barnar da ake yi masu.

Kara karanta wannan

Sojojin Najeriya sun kwato makamai, sun tarwatsa sansanonin 'yan bindiga a Arewa

Mutane na cikin fargaba a Zamfara

‘Yan bindiga sun dasa bam din ne a kan wata gada kusa da hanyar zuwa Dansadau domin hana sojoji motsi.

Mazaunin yankin, Haruna Isyaku, ya bayyana cewa wani direba kadai ne ya yi amfani da hanyar, inda motarsa ta kone kurmus.

Isyaku ya kara da cewa mutane na cikin fargaba saboda tunanin akwai wasu bama baman da aka dasa a hanyoyin yankunan Dansadau da kewaye.

Kalli bidiyon barnar da bam din ya yi a kasa:

Jami'an tsaro sun tono bama bamai

A wani labarin, mun ruwaito cewa jami'an tsaro sun tono bama bamai da 'yan bindiga suka binne a wasu garuruwan jihar Neja da ke Arewacin Najeriya.

Mai magana yawun ƴan sanda, SP Wasiu Abiodun ya ce sun gano waɗannan miyagun makamai ne tsakanin 2021 zuwa 2023.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.