'Yan Majalisar Kano Sun Ajiye Bambancin NNPP da APC a kan Kudirin Haraji
- 'Yan majalisar tarayya da su ka fito daga jihar Kano sun fitar da matsayarsu a kan kudirin harajin gwamnatin tarayya
- An samu dan majalisar APC a cikin wadanda su ka halarci taron da gwamna Abba Kabir Yusuf ya jagoranta a jihar
- Bayan zaman, sun nuna rashin amincewarsu ga abin da kudirin dokar harajin ya kunsa, musamman ga Arewacin Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - 'Yan majalisar tarayya da su ka fito daga jihar Kano, sun ajiye sabanin ra'ayi da su ke da shi a siyasance kan kudirin harajin gwamnatin tarayya.
'Yan majalisa da su ka fito daga jam'iyya mai mulki a kasa ta APC, da NNPP da ke iko da Kano sun hada baki wajen fatali da kudirin Bola Ahmed Tinubu
Hon Sani Adamu Wakili ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa yan majalisar sun zauna da gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Kwamred AbdulSalam Gwarzo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kudirin haraji: 'Yan majalisar Kano sun zauna
Hon Musa Bana ya wallafa a shafinsa na Facebook yadda kusa APC ya hadu da yan majalisar NNPP wajen kin amincewa da kudirin harajin gwamnatin jam'iyyarsa. Daga cikin wadanda su ka halarci zaman akwai Alhassan Ado Doguwa (APC), Injiniya Sagir Ibrahim Koki (NNPP), Sani Wakili (NNPP) Yusuf datti kura (NNPP) da, Gali Panda (NNPP).
Sauran sun hada da Chiroma Gezawa (NNPP), Dan kawu kumbotso (NNPP), Tijjani Abdulkadir Jobe (NNPP), Hassan Husaini Nassarawa (NNPP), Garba Disu Gwale (NNPP), da Kabiru Alhassan Rurum (NNPP).
Matsayar 'yan majalisar Kano kan kudirin haraji
Wasu 'yan majalisa sun amince da hade kai wajen nuna adawa da kudirin da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya bijiro da shi na haraji.
Matsayarsu ta yi daidai da na wasu daga cikin manyan Arewacin Najeriya, daga ciki har da gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum wanda ya fadi illar kudirin.
'Dan majalisa ya fadi amfanin kudurin haraji
A baya, mun wallafa cewa dan majalisar tarayya daga Kano ya ce jama'a ne ba su fahimci abin da kudirin harajin Bola Ahmed Tinubu ya kunsa ba har yanzu.
Hon. AbdulMumin Jibrin Kofa ne ya fadi haka, ya bayyana takaicin yadda aka samu yan majalisa da ke surutai a kan kudirin, bayan a cewarsa, ba su fahimce shi ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng