‘Babu Inda Za a Cutar da Arewa’: Hon. Jibrin Kofa Ya Fayyace Kudirin Haraji
- Dan Majalisar Tarayya daga jihar Kano, Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa ya bayyana yadda tsarin sabon kudirin haraji yake
- Hon. Jibrin Kofa ya ce abin takaici ne yadda wani dan Majalisa yake babatu kan kudirin amma kuma bai fahimci yadda yake ba
- Dan Majalisar ya ce ko kadan wallahi babu inda kudirin zai cutar da Arewa ko kuma talaka kamar yadda ake yadawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Ana ta ce-ce-ku-ce kan sabon kudirin haraji a Najeriya, Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa ya magantu kan lamarin.
Hon. Kofa ya ce wallahi ko kadan babu inda dokar za ta cutar da talaka ko Arewa kamar yadda ake magana.
Hon. Jibrin Kofa ya magantu kan kudirin haraji
Dan Majalisar ya bayyana haka ne a cikin wani faifan bidiyo da DCL Hausa ta wallafa a shafin Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hon. Kofa ya bayyana yadda tsarin yake inda ya ce abin takaici ne sanatan da ke korafi kan kudirin haraji bai ma fahimci abin da ke ciki ba.
Ya ce dokar tana da matukar kyau saboda an cire harajin VAT a harkar ilimi da kayan abinci da bangaren lafiya.
"ita fa wannan dokar tana da kyau, ban da inda aka cutar da talaka ko Arewa ba, a tunani na ban ga ma wata dokar haraji da ta taimakawa talakan Najeriya irin wannan ba."
"Abin da mutane suka damuwa shi ne maganar kaso 60, mu ma jihohin Arewa za su amfana da abin, idan fa aka rage fa ka cutar da Kano."
"Amma ba wani matsala za a iya ragewa misali zuwa 20% ko 30% ko kuma 40% hakan ba wani matsala ba ne."
- Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa
Hon. Kofa ya ce bai yi haka domin cutar da Arewa ba kuma bai taba yin wani abu tsawon shekaru da ya yi a Majalisa saboda cutar da yankin ba sai taimakonta.
Barau Jibrin ya magantu kan sabon kudirin haraji
Kun ji cewa yayin da ake ta ce-ce-ku-ce kan kudirin haraji da Majalisar Tarayya ta yi zama a kai, Sanata Barau Jibrin ya yi karin haske.
Mataimakin shugaban Majalisar ya fayyace yadda lamarin dokar haraji ta ke inda ya ce ba a yi komai ba yanzu ma aka fara muhawara a kai.
Hakan ya biyo bayan caccakar sanatocin Arewa da ake yi musamman shi Barau da ya jagoranci zamanta a ranar Laraba da ta gabata.
Asali: Legit.ng