Shugaba Tinubu Ya Fadi Amfanin da Cire Tallafin Man Fetur Ya Yi Wa Najeriya
- Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sake bayyanawa ƴan Najeriya dalilinsa na cire tallafin man fetur
- Tinubu ya bayyana cewa ya cire tallafin ne domin farfaɗo da tattalin arziƙi ba saboda ya azabtat da ƴan Najeriya ba
- Tinubu ya nuna cewa da bai cire tallafin man fetur ba da tuni tattalin arziƙin Najeriya ya durƙushe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Ondo - Shugaba Bola Tiunbu ya ce cire tallafin man fetur da gwamnatinsa ta yi ba domin azabtar da ƴan Najeriya ba ne.
Shugaba Tinubu ya bayyana cewa ya cire tallafin ne domin ceto ƙasar nan daga durƙushewa baki ɗaya.
Tinubu ya bayyana haka ne a jawabinsa a wajen taron yaye ɗalibai karo na 34 da 35 na jami’ar Fasaha ta tarayya dake Akure, jihar Ondo a ranar Asabar, cewar rahoton jaridar The Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaba Tinubu ya samu wakilcin shugaban jami’ar Ilorin, Farfesa Wahab Egbewole, a wajen taron, rahoton jaridar The Nation ya tabbatar.
Tinubu ya fadi amfanin cire tallafin fetur
Shugaba Tinubu ya yi nuni da cewa manufar cire tallafin man fetur ta fara samar da sakamako mai kyau ga ƙasar nan.
Tinubu ce gwamnatinsa tana da masaniya game da wahalhalun da jama’a ke ciki, amma ya ba da tabbacin cewa daɗi na nan tafe.
"Kamar yadda kuka sani, mun karɓi ragamar mulki ne a daidai lokacin da tattalin arzikinmu ke durƙushewa sakamakon tallafin man fetur da dala."
"Tallafin dai an yi shi ne domin tallafawa talakawa da kuma kyautata rayuwar ɗaukacin ƴan Najeriya."
"Dukkanmu muna sane da cewa talakawan Najeriya sun fi shan wahala kan abin da ya kamata ya a ce ya samar musu da sauƙi da ingantacciyar rayuwa."
"Abin takaici, kyakkyawar rayuwar da muke tunanin muna yi, ta ƙarya ce wacce za ta iya kai ƙasar nan ga rugujewa gaba ɗaya, idan har ba a ɗauki tsauraran matakan gaggawa ba."
"Bisa hakan, ina farin cikin sanar da ku cewa, matakan da muka ɗauka, sun fara haifar da sakamakon da ake buƙata."
- Bola Tinubu
Ba mu gani a ƙasa ba
Sahabi Abdulrahman ya bayyana cewa babu wani amfani da talakan Najeriya ya samu sakamakon cire tallafin man fetur ɗin.
Ya bayyana cewa cire tallafin ba komai ya ƙara ba face jefa mutane cikin wahala.
"Babu wani amfani da muka gani sakamakon cire tallafin mai, face ƙarin wahala da mutane suka tsinci kansu a ciki."
- Sahabi Abdulrahman
Tinubu ya faɗi matsalolin da yake magancewa
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Tinubu ya ce a hankali yana magance matsalolin tattalin arziƙi da gwamnatinsa ta gada.
Shugaba Tinubu ya kuma yarda da matsalolin da ƴan Najeriya ke ciki, sakamakon matakan da gwamnatinsa ta ɗauka.
Asali: Legit.ng