Suna cikin Mawuyacin Hali: Ƴan Fashi Sun Farmaki Tawagar Ƴan Ƙwallon Ƙafa a Arewa
- 'Yan fashi sun farmaki tawagar El-Kanemi Warriors a Rijiyar Malam, kan hanyar Jos-Bauchi, inda sun jikkata 'yan wasa da jami'ai
- An kai 'yan wasan kwallon da suka jikkata zuwa asibitin koyarwa na ATBU domin kula da su, sannan aka kai rahoto ga 'yan sanda
- Rundunar 'yan sandan Bauchi ta tabbatar da lamarin, ta kuma ce za a kamo masu laifi bisa umarnin CP Auwal Musa Muhammad
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Bauchi - 'Yan fashi sun kai hari kan motar tawagar 'yan wasan El-Kanemi Warriors a kauyen Rijiyar Malam, kan hanyar Jos-Bauchi a jihar Bauchi.
An rahoto cewa 'yan fashin dauke da makamai sun jikkata 'yan wasa da jami'ai da dama tare da yin awon gaba da wasu kayansu.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa tawagar na kan hanyarsu ta zuwa wasan gasar kwallon kafa lokacin da lamarin ya faru.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda 'yan fashi suka tare 'yan kwallon
Mataimakin mai ba 'yan wasan horo, Suleiman Abdullahi, ya ce
"Mun fada komar 'yan fashin da misalin karfe 12:45 na daren ranar Asabar yayin dawowa daga Jos zuwa Maiduguri.
'Yan fashin sun rufe motoci biyu tare da wata mota kirar saloon, suka bude wuta, sannan suka tsayar da mu suka fitar da kowa daga cikin motocin."
Halin da 'yan wasan El-Kanemi suka shiga
Ya kara da cewa:
"'Yan fashin sun farmake mu da adda da sanda, suka kwace mana kudi, wayoyi, da wasu muhimman kayayyaki.
"Fiye da mutum goma cikin 'yan wasan da jami'ai sun jikkata sakamakon wannan harin."
Bayan faruwar lamarin, an kai wadanda suka jikkata zuwa Asibitin koyarwa na Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi domin samun kulawa.
Kungiyar ta kuma ce an kai rahoton lamarin ga ofishin 'yan sanda na GRA a Bauchi kafin tawagar ta wuce Maiduguri.
'Yan sanda sun yi magana kan harin
Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan Bauchi, SP Ahmed Wakil, ya tabbatar da harin, yana mai cewa sakataran kungiyar, Dahiru Bala, ne ya kai rahoton ga 'yan sanda.
SP Wakil ya ce:
“A halin yanzu, kwamishinan ‘yan sanda, Auwal Musa Muhammad, ya ba da umarnin tashi tsaye domin kamo masu laifin."
Ya kuma bayyana cewa wadanda aka kwacewa kayayyaki za su iya tuntubar hukumar ta hanyar manhajar “Rescue Me” domin gano wayoyinsu da aka sace.
Dan kwallon Najeriya ya rasu
A wani labarin, mun ruwaito cewa fitaccen dan wasan kwallon Najeriya, Gift Atulewa ya rasu yana da shekaru 38 sakamakon abin da ake zargi da ciwon zuciya.
An ce watan da ya gabata ne aka birne matarsa da ta rasu, wanda ake zargin hakan ya kara jawo tabarbarewar rashin lafiyarsa da zama ajalinsa a karshe.
Asali: Legit.ng