"Zan Magance Matsalolin Najeriya," Tinubu Ya Bayyana Shirin da Ya Yiwa Talakawa

"Zan Magance Matsalolin Najeriya," Tinubu Ya Bayyana Shirin da Ya Yiwa Talakawa

  • Shugaba Bola Tinubu ya jaddada aniyarsa ta magance matsalolin Najeriya ta hanyar noma, wanda ya kira hanyar fadada arziki
  • Ya ce karin jami’o’in noma zai taimaka wajen rage dogaro da man fetur, tare da samun nasarar samar da abinci mai dorewa
  • Tinubu ya tabbatar da cewa, tare da aiki tukuru da goyon bayan masana noma, Najeriya za ta rage dogaro da shigo da kayan abinci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abia - Shugaba Bola Tinubu a ranar Asabar ya sake jaddada aniyarsa ta magance matsalolin Najeriya, da ragewa talaka radadi ta hanyar dabarun tattalin arziki.

Da yake magana a Umuahia a bikin yaye dalibai karo na 12 na jami’ar Noma ta Michael Okpara, ya nuna noma a matsayin muhimmiyar hanya ta fadada tattalin arziki.

Kara karanta wannan

Dokar haraji: Sanatocin Arewa sun yi ganawar sirri bayan kudirin ya tsallake karatu na 2

Tinubu ya yi magana kan amfanin noma a ci gaban tattalin arzikin Najeriya
Shugaba Tinubu ya bayyana yadda zai yi amfani da noma wajen bunkasa tattalin arziki. Hoto: @PBATMediaCentre
Asali: Twitter

Habaka noma domin abinci da tattalin arziki

Tinubu ya ce gwamnatinsa ta kara yawan jami’o’in noma don karfafa bangaren abincida rage dogaro da kudaden man fetur a Najeriya, a cewar rahoton Arise News.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da ya samu wakilcin, Dr. Deola Lordbanjou daga ma’aikatar noma ta tarayya, Tinubu ya jaddada muhimmancin masana noma wajen magance rashin wadatar abinci.

"Wannan kasa tana bukatar masana noma a matsayin masu sauya fasalin tattalin arziki don kawar da yunwa da fadada tattalin arziki."

- A cewar Tinubu.

Inganta ilimi domin bunkasa tattali

Ya kara da cewa za a ci gaba da bukatar kwarewar fasaha har sai Najeriya ta cimma burinta na wadatar abinci mai dorewa da dogaro da kai.

Tinubu ya bayyana cewa ilimi mai inganci yana da muhimmanci wajen warware matsalolin zamantakewa da tattalin arziki ta hanyar sabbin dabaru.

Don inganta samun damar ilimi, Punch ta rahoto Tinubu ya ce gwamnatinsa ta kafa asusun lamunin ilimi na kasa (NELFund) don bayar da lamuni ga dalibai cikin sauki.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta fadi adadin fetur da matatar Fatakwal za ta samar a kullum

Amfanin jami'o'in noma ga Najeriya

Shugaban ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa wannan shiri zai rage wa dalibai da iyaye nauyin kudade, tare da karfafa yaki da talauci da bunkasar tattalin arziki.

Tinubu ya kara bayanin cewa kara yawan jami’o’in noma wata dabara ce da aka tsara don tabbatar da Najeriya ta dogara da kanta wajen samar da abinci.

Ya bayyana tabbacin cewa da himma, Najeriya za ta rage dogaro da shigo da abinci kuma ta cika bukatun al’ummarta na abinci na yau da kullum.

Tinubu ya dauki matakin gyara tattali

A wani labarin, mun ruwaito cewa Shugaban Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa ta karbi mulkin Najeriya a cikin durkushewar tattalin arziki.

Shugaban kasar ya bayyana cewa wannan ta sa gwamnatinsa ta dauki wasu tsauraran matakai da yan Najeriya ke kokawa da su a fadin kasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.