Yan Arewa Sun Hada Kai Babu Bambanci, Sun Taso Barau Jibrin gaba kan Kudirin Haraji

Yan Arewa Sun Hada Kai Babu Bambanci, Sun Taso Barau Jibrin gaba kan Kudirin Haraji

  • A wannan karo yan Arewa sun hada kai ba tare da bambanci ba domin kalubalantar sabon kudirin haraji
  • Kungiyoyi da matasa da sauran al'umma sun nuna kiyayyarsu ga kudirin da suke ganin zai nakasa yankin Arewa
  • Daga cikinsu akwai Majalisar Matasan Arewa inda ta caccaki Sanata Barau Jibrin da ya jagoranci zaman Majalisar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Maganar sabon kudirin haraji ta jawo ce-ce-ku-ce a Arewacin Najeriya gaba daya.

Mataimakin shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin ya sha suka kan kudirin haraji da ake ganin koma-baya ne ga yankin Arewa.

Yadda yan Arewa suka taso Sanata Barau kan kudirin haraji
Matasan Arewa sun caccaki Sanata Barau Jibrin kan kudirin haraji. Hoto: Barau I Jibrin.
Asali: Twitter

Haraji: Matasan Arewa sun soki Sanata Barau

Rahoton Vanguard ya ce yan Arewa sun hada kai duk da mambance-bambancen da ake da su a yankin domin kalubalantar kudirin.

Kara karanta wannan

'A ji ra'ayin jama'a': Atiku ya magantu kan kudirin haraji, ya ba Majalisa shawara

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majalisar Matasan Arewa ta caccaki Sanata Barau Jibrin kan wannan kudirin haraji da ya tsallake karatu na biyu karkashin jagorancinsa.

An dura kan sanata Barau ne duba da cewa shi ya jagoranci zaman Majalisar da kudirin harajin ya tsallake karatu na biyu duk da cewa daga Arewa yake.

Shugaban kungiyar, Ali Mohammed Idris ya ce Sanata Barau ba wakiltar yankin Arewa yake yi ba kan kudirin harajin, cewar Leadership.

'Ba ka kishin yankinka' - Majalisar Matasan Arewa

"A madadin shugabannin Majalisar Matasan Arewa a jihohi 19, muna Allah wadai da kai kan tabbatar da kudirin haraji da ya tsallake karatu na biyu."
"Wannan kudirin haraji babu abin da zai yi sai ruguza yankin Arewa ta fannin tattalin arziki da kuma kasuwanci."
"Goyon bayanka kan tabbatar da harajin ya nuna rashin kishin mazabarka da jihar Kano da ma Arewacin Najeriya."

- Majalisar Matasan Arewa

Barau ya yi karin haske kan haraji

Kara karanta wannan

'Tinubu zai yi rugu rugu da tattalin arzikin Arewa': Bulama Bukarti ya fayyace kudirin haraji

A baya, kun ji cewa Sanata Barau Jibrin ya yi magana kan sabon kudirin haraji da ake ta ce-ce-ku-ce a kai.

Sanata Barau ya ce ban da al'umma har cikin Sanatoci akwai wadanda ba su fahimci abin da ke cikin dokokin ba.

Ya tabbatar da cewa domin kudirin ya tsallake karatu na biyu ba shi ne ya zama doka ba, yanzu aka fara muhawara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.