2027: 'Yadda Atiku, Peter Obi da Sauransu Suka Shirya Kawo Karshen Mulkin Tinubu'
- Shugaban kungiyar 'Citizens Coalition' a Najeriya ya yi magana kan hadakar jam'iyyun adawa a zaben 2027
- Shugaban kungiyar, Kelly Agaba ya ce tabbas akwai haske kan tafiyar da ake yi na jam'iyyun adawa da kuma kungiyoyi
- Agaba ya tabbatar da cewa a yanzu haka akwai gwamnoni 15 da suka shiga tafiyar da wasu masu ruwa da tsaki a APC a Arewa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Wani mai fashin baki kan harkokin siyasa ya magantu kan shirin haɗaka da ake yi game da zaben 2027.
Kelly Agaba ya ce akwai haske a kokarin hadakar Atiku Abubakar da Peter Obi da sauransu kan kwace mulkin Bola Tinubu.
Atiku da Obi sun shirya kifar da Tinubu
Agaba wanda shi ne shugaban kungiyar 'Citizens Coalition' ya fadi haka ne yayin hira ta musamman da jaridar Legit a jiya Asabar 30 ga watan Nuwambar 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dan gwagwarmayar ya ce tabbas akwai hadakar jam'iyyun adawa da kungiyoyi mai ƙarfi musamman kan zaben 2027.
A cikin hirar, Agaba ya tabbatar da cewa a yanzu haka akwai gwamnoni 15 da suka shiga tafiyar domin a dama da su wurin kalubalantar Bola Tinubu.
Yadda aka shirya kalubalantar Tinubu a 2027
"Tabbas akwai shirin haɗaka mai ƙarfi tsakanin jam'iyyu da kungiyoyi, yanzu haka gwamnoni 15 sun shiga tafiyar."
"Kun sani babu wanda zai yi takara shi kadai kuma ya ci zabe, yanzu haka masu ruwa da tsaki a APC na Arewacin Najeriya sun shiga tafiyar su ma."
"Yanzu APC da Bola Tinubu za a rage musu karfi zuwa jam'iyyar yanki kawai."
- Kelly Agaba
Ana hasashen 2027, Atiku ya gana da Obi
A wani labarin, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya karbi bakuncin Peter Obi a gidansa.
Atiku ya gana da dan takarar shugaban kasa a LP ne a gidansa da ke jihar Adamawa a jiya Asabar 30 ga watan Nuwambar 2024.
Wanann na zuwa ne yayin da ake ta hasashen cewa jam'iyyun adawa na kokarin yin haɗaka domin kwace mulkin Bola Tinubu.
Asali: Legit.ng