Kazamar Fada Ta Barke tsakanin Yaran Turji da 'Yan Banga, Manoma Sun Shiga Yanayi

Kazamar Fada Ta Barke tsakanin Yaran Turji da 'Yan Banga, Manoma Sun Shiga Yanayi

  • Rahotanni sun tabbatar da cewa kazamar fada ta barke tsakanin yan banga da kuma yaran Bello Turji
  • An yi arangamar a yankin Fadamar Tara da ke jihar Zamfara inda yan ta'addan suka yi kokarin kwace iko a yankin
  • Sai dai yan banga sun kawowa al'ummar yankin da manoma dauki saboda kare mutane da ke rayuwa a wurin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Zamfara - An shiga cikin fargaba yayin da fada ta barke tsakanin yaran Bello Turji da yan banga a Arewacin Najeriya.

Ana zargin dakarun Turji sun farmaki manoma a Fadamar Tara a jihar Zamfara inda suka fatattake su.

An daure tsakanin yan banga da yaran dan ta'adda, Bello Turji
Fada ta barke yayin da yan banga suka gwabza da yaran Bello Turji a jihar Zamfara. Legit.
Asali: Original

Hafsan sojoji ya gargadi Turji, yan ta'adda

Rahoton Zagazola Makama shi ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa a yau Asabar 30 ga watan Nuwambar 2024.

Kara karanta wannan

Kaduna: Gwamna Uba Sani ya karbi kasurguman yan bindiga da suka tuba

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na zuwa ne kwanaki ƙadan bayan sabon mukaddashin hafsan sojoji a Najeriya, Laftanar-janar Olufemi Oluyede ya sha alwashin kakkabe yan ta'adda.

Laftanar-janar Olufemi ya gargadi Bello Turji da yan ta'adda su shirya domin a wannan lokaci ba za su ji ta dadi ba ko kadan karkashin ikonsa.

Zamfara: An yi fada da yaran Bello Turji

Rahoton ya ce kazamar fada ya kauye tsakanin yan banga da kuma wasu yan ta'adda da ake kyautata zaton yaran Bello Turji ne.

Wani shaidan gani da ido ya ce yan ta'addan sun tilasta manoman barin yankin inda suka nemi karbe ikon wurin.

Daga bisani, yan banga sun kawo dauki domin kalubalantar yan ta'addan da kwace ikon yankin da kuma kare al'umma.

Wasu majiyoyi sun tabbatar da cewa ana cigaba da arangama tsakanin bangarorin biyu.

Sai dai har zuwa wannan tattara wannan rahoto ba a samu tabbacin yawan raunuka da rasa rai game da arangamar ba.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya tsoratar da Tinubu, ana zargin EFCC ta fara bincike domin karya shi

Turjj ya gwabza fada da jami'an tsaro

A wani labarin mai kama da wannan, Mun samu rahotanni da ke tabbatar da cewa ana kazamar fada tsakanin Bello Turji da dakarun sojoji a jihar Sokoto.

Sojojin da yan Gatawa sun kaure da yan ta'addan karkarshin jagorancin Bello Turji da safiyar yau Talata a Sokoto.

An tabbatar da an fara fadan tun misalin karfe 6.00 na safe, ana cigaba da fafatawa har zuwa lokacin tattara rahoton.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.