'Za Ku Yabawa Tinubu nan gaba': Dan Majalisar Tarayya daga Arewa kan Kudirin Haraji
- Dan Majalisar Tarayya daga yankin Arewacin Najeriya ya yabawa Bola Tinubu kan sabon kudirin haraji da ke gaban Majalisa
- Hon. Philip Agbese daga jihar Benue ya ce yan Najeriya za su yabawa Tinubu daga baya kan wannan kokarin da yake yi
- Agbese ya kuma yabawa hukumar tattara haraji ta FIRS kan irin sababbin dabarun samun kuɗi da take kawowa a kasar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Benue - Dan Majalisar Tarayya daga jihar Benue, Philip Agbese ya fadi alfanun kudirin haraji da Bola Tinubu ya kawo.
Agbese ya tabbatar da cewa yan Najeriya za su dawo suna yabon Shugaba Bola Tinubu kan kudurinsa game da tattalin arziki.
Dan Majalisa ya yabawa Tinubu kan kudirin haraji
Dan Majalisar ya bayyana haka ne a yau Asabar 30 ga watan Nuwambar 2024 yayin ganawa da yan jaridu, cewar The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Agbese ya yabawa shugaban hukumar tattara haraji ta FIRS, Zach Adedeji da kwamitin Gwamnatin Tarayya kan inganta haraji a kasar.
Ya ce sun yi abin da ya dace wurin zakulo irin wadannan cigaba da ake bukata domin inganta tattalin arzikin Najeriya, Punch ta ruwaito.
Haraji: Hon. Agbese ya yabawa hukumar FIRS
"Abin da hukumar FIRS ke yi a yanzu abin a yaba ne, hukumar ta samar da makudan kudi fiye da yadda aka gindaya mata karkashin jagorancin Mr Adedeji."
"Yan Najeriya za su zo suna yabawa Tinubu lokacin da aka tabbatar da dokar domin Gwamnatin Tarayya ta samu kudade."
"Za a yi amfani da kudin wurin samar da ababan more rayuwa da manyan ayyuka a kasa saboda kudin da za a samu dalilin harajin."
"Sannan za a samu yawaitar ayyukan yi a tsakanin al'umma wanda zai dakile matsalar talauci a Najeriya."
- Philip Agbese
Bulama ya magantu kan kudirin harajin Tinubu
Kun ji cewa fitaccen lauya, Bulama Bukarti ya bayyana illar sabon kudirin haraji ga tattalin arzikin Arewacin Najeriya.
Bukarti ya ce tun a shekarar 1999 ba a taba yin wata doka ta za ta yi rugu-rugu da Arewa ba irin wannan kudirin haraji.
Asali: Legit.ng